Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana taron harkar noma a Kano dake tarayyar Najeriya


Nigeria
Nigeria

Taron na yini hudu ya tattaro duk kwamishanonin noma na jihohi 36 da yankin Abuja da manyan jami'an ma'aikatar noman kowace jiha.

A wurin taron akwai kwararru akan harakar noma tare da shugabannin cibiyoyin nazarin aikin noma daga sassan Najeriya.

Kwamishanan noma na jihar Kano, jihar da ta sauki bakin Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana makasudin taron. Yace kowace shekara akan zauna a tattauna akan harkokin noma da yadda za'a kawo cigaba. Taron ya zama tamkar majalisa ce ta koli akan harkokin noma.

Taron zai karkata akala ne wajem tattauna hanyoyin da aikin noma da zasu cike gibin da Najeriya ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki sanadiyar faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Dr. Shehu Ahmad babban sakatare a ma'aikatar gona ta tarayya wanda ya wakilci ministan noma ya fada cewa dama can aikin noma ke ba mutane ayyukan yi da habaka tattalin arziki. Shi yake sa matasa suna samun aikin yi. Idan kasar ta saka jari sosai cikin ayyuka da harkokin noma kasar zata manta da batun man fetur.

Mahalarta taron daga jihohi sun bayyana kyautata zaton aikin noma zai habaka tattalin arzikin kasar.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG