Laraba, Agusta 20, 2014 Karfe 06:48

Afirka

Ana Zaman Makoki Na Kwana Uku A Kasar Ivory Coast

Wani soja tsaye kusa da komotsan wadanda aka tattake a turmutsutsu
Wani soja tsaye kusa da komotsan wadanda aka tattake a turmutsutsu
Kasar Ivory Coast ta fara zaman makoki na tsawon kwana uku jiya Laraba bayan turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 60 a jajibirin sabuwar shekara gabilinsu matasa.

An murkushe  dama daga cikin mamatan ne ko aka matse su suka kasa lunfashi lokacin da lamarin ya faru a Abidjan ranar Talata.

Masu gudanar da bincike basu da tabbacin abinda ya haddasa turmutsutsun da ya faru kusa da wani babban filin wasa inda dubun dubatan mutane suka taru domin kallon wasan wuta.

A shekara ta dubu biyu da tara, turmutsutsu a wannan filin wasan ya yi sanadin mutuwar mutane 22.

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio Shirin Safe        MP3

Audio Shirin Rana       MP3

Audio Shirin Dare       MP3

Audio Mu Tattauna       MP3