Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 12:14

  Labarai / Afirka

  A Kenya ana Ci Gaba Da Ayyukan Ceton Jiragen Sojan Uganda.

  Masu aikin ceto a Kenya suna ci gaba da kokarin kaiwa ga inda jiragen soja masu saukar ungulu na kasar Uganda suka yi hadari

  A wan nan hoto da rundunar mayakan Kenya ta bayar ana nuna ceton matukin jirgin Uganda da yayi hadari.A wan nan hoto da rundunar mayakan Kenya ta bayar ana nuna ceton matukin jirgin Uganda da yayi hadari.
  x
  A wan nan hoto da rundunar mayakan Kenya ta bayar ana nuna ceton matukin jirgin Uganda da yayi hadari.
  A wan nan hoto da rundunar mayakan Kenya ta bayar ana nuna ceton matukin jirgin Uganda da yayi hadari.
  Masu aikin ceto a Kenya suna ci gaba da kokarin kaiwa ga inda jiragen soja masu saukar ungulu na kasar Uganda  suka yi hadari a kan dutsen Kenye dake tsakiyar kasar.
  Jami’an rundunar sojojin Kenya sun fada yau talata cewa sun hango inda baraguzan jiragen suke daga sama, amma basu san makomar wadanda suke jiragen ba ahalin yanzu.
  A wan nan hoto daga hanun dama sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce da shugaban kasar kenya Mwai Kibaki.A wan nan hoto daga hanun dama sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce da shugaban kasar kenya Mwai Kibaki.
  x
  A wan nan hoto daga hanun dama sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce da shugaban kasar kenya Mwai Kibaki.
  A wan nan hoto daga hanun dama sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce da shugaban kasar kenya Mwai Kibaki.

  Ranar litinin masu aikin ceto sun gano jirgi na ukun, wadda yayi saukar gaggawa kan dutsen na  Kenya. An ceto duka mutane bakwai da suke cikin wan nan  jirgin.
  Jami’an Kenya suka ce masu bincike suna aza laifin hadarin kan munin yanayi.
  Tun litinin ake samun rahotanni masu sabani da juna kan makomar jiragen. Rahotannin farko sun nuna cewa an gano duka jiragen uku, kuma tuni har wai an ceto duka jami’ai dake cikin jirgin.
  Jiragen yakin sojan Ugandan masu saukar ungulu, suna kan hanyar zuwa  Somalia ne domin kara karfi ga rundunar da tarayyar Afirka ta tura kasar, domin ayyukan kiyaye zaman lafiya.
  Jirgi na hudu ya sauka lafiya a wani sansanin soja dake arewa maso gabashin Kenya.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye