Asabar, Nuwamba 28, 2015 Karfe 22:59

Labarai / Sauran Duniya

Ecuador Ta Baiwa Julius Assange Mafaka.

Hotun Julian Assange Mutuminda ya kafa dandalin WikiLeaks, mai fallasa sirrin gwamnati da kungiyoyi.Hotun Julian Assange Mutuminda ya kafa dandalin WikiLeaks, mai fallasa sirrin gwamnati da kungiyoyi.
x
Hotun Julian Assange Mutuminda ya kafa dandalin WikiLeaks, mai fallasa sirrin gwamnati da kungiyoyi.
Hotun Julian Assange Mutuminda ya kafa dandalin WikiLeaks, mai fallasa sirrin gwamnati da kungiyoyi.
Alhamis din nan ne ministan harkokin wajen Ecuador, Ricardo Patino, ya bada sanarwar haka a Quino, yana mai cewa lafiya da tsaron Assange yana cikin hadari. Yace ba  za a yiwa Assange adalci ba idan aka mikashi hanun Amurka.

Ministan harkokin wajen Britaniya William Hague, yace Ingila ba  zata baiwa Assange damar barin kasar ba, kuma a shirye take wajen ganin ta mika shi ga kasar Sweden.
'Yansandan Ingila a ofishin jakadancin Ecuador dake kasar.'Yansandan Ingila a ofishin jakadancin Ecuador dake kasar.
x
'Yansandan Ingila a ofishin jakadancin Ecuador dake kasar.
'Yansandan Ingila a ofishin jakadancin Ecuador dake kasar.

Mahukuntan Sweden suna neman Assange saboda ya amsa tambayoyi kan  zargin ya tilastawa wata mace lalata da shi. Assange ya musanta wan nan zargi.
Bayanda Ecuador ta yanke wannan shawara, Sweden ta gayyaci jakadan Ecuador dake kasar, a wani mataki na difilomasiyya. kakakin gwamnatin Sweden yace gwamnatin kasar  “ba zata lamunta ba”  ganin Ecuador tana kokarin katsalandan cikin harkokin shari’ar kasar.

Daya daga cikin lauyoyin Assange, yayi kira ga mai gabatar da kara na Sweden  yazo London ya yiwa Assange tambayoyi, ganin yanzu babu sauran zarafin mutuminda yake baiwa kariya zai je Sweden, saboda yanzu an bashi mafaka.

Assange yana cikin ofishin jakdancin Ecuador tun cikin watan Yuni, bayanda ya sha kaye a kotu a kokarinsa na hana hukumomin kasar mika shi ga hukumomin Sweden.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye