Talata, Satumba 16, 2014 Karfe 19:27

Sauran Duniya

Libya Ta Kama Mutane Hudu Dangane Da Harin Da Aka Kai Ofishin Jakadancin Amurka.

Masu zanga zanga da ta yi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurka A LibyaMasu zanga zanga da ta yi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurka A Libya
x
Masu zanga zanga da ta yi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurka A Libya
Masu zanga zanga da ta yi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurka A Libya
Jami’an Libya suka ce hukumomin kasar sun kama mutane hudu dangane da mummunar tarzomar da aka yi cikin makon nan kan karamin ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi, a dai dai wannan lokacin ne kuma hukumomi suke shirin fuskanatar karin tarzoma a fadin gabas ta tsakiya, saboda wani silima na batunci kan musulunci.

Hukumomin Libya basu bada karin bayani kan mutanen hudu da aka kama dangane harin da aka kai ranar talata wadda yayi sanadiyyar mutuwar jakada Christopher Stevens, da wasu jami’ai uku.

Hukumomin leken asirin Amurka suna binciken zargin da hanun magoya bayan kungiyar al-Qaida  a kai wannan hari. Duk da haka suka  ce basu da wani sheda mai karfi kan wannan zargi.

Ahalinda  ake ciki kuma, an kashe ‘yan zanga zanga hudu a Yemen, lokacind a wani gungun jama’a suka farwa ofishin jakdancin Amurka a jiya Alhamis.

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio  Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio  Shirin Hantsi:         0700 - 0730 UTC

        Shirin Rana                1500 - 1530 UTC

Audio        Rumbun Shiri                      Live  

        Shirin Dare                2030 - 2100 UTC

Audio        Rumbun Shiri                      Live