Asabar, Agusta 29, 2015 Karfe 13:36

Zaben 2012 a Amurka

Mitt Romney Yana Kokarin Sake Karkato Yakin Neman Zaben Shugabancin Amurka Da Yake Yi Ya Mike Bayan.....

Mitt Romney mutuminda yake takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Republican.
Mitt Romney mutuminda yake takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Republican.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Mitt Romney, yayi kokarin sake karkato yakin neman zaben da yake yi  ya dawo kan hanya, bayanda wani fefen vidiyo da  aka dauka a sirce, ya kufularda  magoya bayan shugaba Obama sosai.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Mitt Romney da uwargidansa Ann Romney.Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Mitt Romney da uwargidansa Ann Romney.
x
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Mitt Romney da uwargidansa Ann Romney.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Mitt Romney da uwargidansa Ann Romney.

Anji Mr. Romney cikin vidiyon yana cewa kashi 47 cikin dari na masu zabe a Amurka masu goyon bayan shugaba Obama basa biyan haraji, kuma sun dage hakkinsu ne  a basu inshoran kiwon lafiya da wasu kayan more  rayuwa ba tareda sun dauki nauyin hakkinda ya rataya a wuyarsu ba.

Jiya talata Mr. Romney ya amince bai tsara maganar  da  yayi da kyau ba, duk da haka yace  zai ci gaba da yakin neman ganin an rage karfin da girman gwamnatin tarayyar Amurka.

Kakakin fadar White House Jay Carney yace shugaba Obama, baya kallaon mutane da suke samun tallafin gwamnati kamar dalibai a matsayin mutane da aka “zalunata ba”.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti