Talata, Mayu 26, 2015 Karfe 02:30

Najeriya

Fada Tsakanin JTF Da Boko Haram Ya Kaure A Potiskum

An yi ta jin fashe-fashe da harbe-harbe tun daga karfe 6 na safiyar yau laraba a garin na Potiskum dake Jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya

Sojoji su na wucewa ta jikin wasu gidajen da aka kona a Maiduguri, 8 Oktoba, 2012
Sojoji su na wucewa ta jikin wasu gidajen da aka kona a Maiduguri, 8 Oktoba, 2012
Fashe-fashe da kuma karar harbe-harbe sun jijjiga wani gari yau laraba a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kwana biyu bayan da aka kashe mutane 24 a wani tashin hankali a wannan yanki.

Mazauna garin Potiskum a Jihar Yobe, sun ce an fara gwabzawa da misalin karfe 6 na safe. Wani gidan telebijin mai suna Channels TV yace dakarun tsaron Najeriya su na gwabzawa ne da ‘ya’yan kungiyar na ta Boko Haram.

Rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF ta fada cewa a ranar litinin da maraice ta kashe ‘yan Boko Haram su 24 ta kuma kama makamai masu yawa a birnin Maiduguri. Wata sanarwa ta ce ‘yan Boko Haram din su na buya a cikin gidajen fararen hula domin kai farmaki a kan dakarun JTF.

Shaidu sun zargi rundunar JTF da laifin cin zarafin jama’a a fadan da take yi da ‘yan Boko Haram. A makon jiya, rundunar ta musanta zargin cewa sojoji sun kashe mutane akalla 30, suka kona kantuna da gidajen jama’a a Maiduguri, a wani matakin daukar fansar wani harin bam da aka kai musu.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta fada a makon jiya cewa da alamun dukkan bangarorin sun aikata laifuffuka na cin zarafin bil Adama.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Kabiru Badu Daga: Kano
17.10.2012 16:30
Rigingimun da suka addabi jama'a a potiskum da sauran sassan arewa maso gabacin nijeriya musiba ce babba, Ya Allah ka kawo mana karshen wannan al'amarin

Ra’ayoyinku da 2015 Zabe

Yaya zabe yake gudana a wajen zaben ku?

Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

#zaben2015

Muna bukatar hotuna da bidiyon garin ku, ko unguwar ku, da rumfunan zaben ku, da ma duk wani abun da ya shafi zabe tsakanin APC da PDP. Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

Karin Bayani akan VOA Hausa Facebook