Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 06:14

Najeriya

An Kai Harin Kunar-Bakin-Wake Kan Coci A Kaduna

An kashe mutane 7 cikin wannan coci, yayin da aka kashe wasu mutanen 2 a hare-haren ramuwar gayya da suka biyo bayan harin kunar-bakin-waken.

Majami'ar St. Rita dake Kaduna, a bayan harin bam na kunar-bakin-wake, lahadi 28 Oktoba, 2012.
Majami'ar St. Rita dake Kaduna, a bayan harin bam na kunar-bakin-wake, lahadi 28 Oktoba, 2012.
Hukumomin Najeriya da kuma wasu shaidun gani da ido sun ce wani dan kunar-bakin-wake ya kara motar da aka zuba nakiya ciki da wata majami’a a garin Kaduna na arewacin kasar, ya kashe mutane 7, ya kuma haddasa hare-haren ramuwar gayyar da suka yi sanadiyyar mutuwar wasu mutanen su biyu.

Dan harin ya abka kan majami’ar St. Rita dake unguwar Malali a Kaduna cikin wata motar jif a lokacin da aka taru ana ibada yau lahadi da safe. Masu aikin gaggawa sun garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibitoci. Shaidu sun ce a bayan harin, Kiristoci matasa da suka fusata sun fito kan tituna dauke da adduna da sanduna inda suka lakkada duka ma wasu Musulmi biyu ‘yan acaba har lahira.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai hari kan wannan majami’a.

A can baya, kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai harin bam da na bindiga a kan majami’u da dama cikin shekara guda da ta shige. A watan Yuni, kungiyar ta dauki alhakin hare-haren bam uku kan majami’u a jihar Kaduna, wadda ke tsakiyar kasar a dab da inda Najeriya ta rabu biyu tsakanin arewaci inda Musulmi ke da rinjaye da kuma kudanci inda Kiristoci ke da rinjaye.

Hukumomin Najeriya su na dora ma kungiyar Boko Haram alhakin kisan mutane fiye da dubu daya da dari biyar, ciki har da ‘yan sanda da jami’an gwamnati kama daga shekarar 2009. Da alamun ‘yan kungiyar su na enma ne su kafa irin ta su fassarar tsarin shari’ar Musulunci a arewacin Najeriya.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Hassan Daga: Kafanchan
05.11.2012 08:59
Wanda ya gina ramin mugunta ya kwana da sanin zai fada a chiki ko bajima ko badade. kana gidan gilashi kana wasan jifa.


by: Musa Daga: Kafanchan
29.10.2012 10:53
Nafi kuka da wadanda suke ba maharan nan mafaka.


by: Maccido musa Daga: Sokoto state, kware L/G
28.10.2012 20:43
Muna rokon Allah ya zaunarda kasarmu lafiya.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti