Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Gurneti a Kenya


Jami’ai a gabashin Kenya sun ce wani harin gurnatin da aka kai kan wata Majami’a yau Lahadi, ya raunata akalla mutane 8, wasu da tsanani sosai.

Jami’ai a gabashin Kenya sun ce wani harin gurnatin da aka kai kan wata Majami’a yau Lahadi, ya raunata akalla mutane 8, wasu da tsanani sosai.

Shugaban Majami’ar ta Utawala da ke garin Garissa na cikin wadanda abin ya rutsa da su, da kuma wasu ‘yan sanda da dama. An kai harin ne kan Majami’ar da ke harabar rukunin gidajen ‘yan sanda.

Take dai babu wanda ya dau alhakin kai harin.

‘Yan bindiga sun sha auna Kenya tun bayan da kasar ta tura sojojinta zuwa Somaliya don taimakawa a yakin da ake da al-Shabab mai alaka da al-Qaida. Wasu tagwayen hare-hare kan wasu Majami’u a Garissa cikin watan Yuli sun hallaka mutane wajen 20.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG