Litinin, Agusta 31, 2015 Karfe 01:31

Labarai / Sauran Duniya

Yakin Neman Zabe Ya Kankama A Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama
Ibrahim Garba
Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton ya kasance a tawagar yakin neman zabe da Shugaba Barack Obama da daren jiya Asabar a yayin da ake shiga ranaku na karshe na yakin neman zaben Shugaban Amurka da za a yi jibi Talata.
 
Mr. Clinton, wanda har muryarsa ta shake saboda galabaitar da ya yi wajen kanpe wa Mr. Obama, y ace ya sadaukar da muryarsa ga aiki wa Shugaban kasar. Sama da mutane 24,000 ne su ka hallara a dandalin Bristow, na jihar Viginia don sauraran tsoho da kuma shugaba mai ci din.
 
Mr. Obama da mai kalubalantarsa na jam’iyyar Republican na ta kai kawo a kasar a daidai lokacin da lokacin yakin neman zaben ke karewa.
 
Kuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna cewa ‘yan takarar biyu sun yi kankankan a muhimman jihohin Colorado da Florida da Ohio da kuma Virginia. Shugaba Obama ya dan zarce a Ohio da Virginia a yayin da Mr. Romney ked an gaba a Colorado kuma sun yi kunnen doki a Florida.
 
Wadannan jihohin 4, su ake wa lakabi da jihohi masu tasiri, da ke da muhimmanci wajen samun kuri’u 270 da ake bukata don cin zaben shugaban kasar ta Amurka.


A yayin wani gangamin yakin neman zabe a muhimmiyar jiha ta New Hampshire, Mr Romney ya sake caccakar abubuwan da Shugaba Obama ya cimma, inda ya gaya wa magoya bayansa cewa Shugaba Obama ya kasa cika alkawuran da ya yi.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti