Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takara Su Na Kai Gwauro Da Mari A Fadin Amurka


Tsohon shugaba Bill Clinton (hagu) yana gabatar da shugaba Barack Obama a wajen yakin neman zabe a garin Bristow a Jihar Virginia ran asabar.
Tsohon shugaba Bill Clinton (hagu) yana gabatar da shugaba Barack Obama a wajen yakin neman zabe a garin Bristow a Jihar Virginia ran asabar.

Ana saura 'yan sa'o'i kafin zabe, shugaba Barack Obama da Mitt Romney suna yakin neman zabe gadan-gadan a jihohin da har yanzu ba fitaccen gwani.

Ana saura kwanaki biyu kafin zabe, shugaba Barack Obama da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney, su na kai gwauro da mari a fadin Amurka, inda dukkansu biyu ke yakin neman zabe a jihohin da har yanzu ba a san gwani ba, inda kuma nan ne za a iya tantance wanda zai lashe zaben.

A gangaminsa na farko lahadi, shugaba Obama ya ziyarci Jihar New Hampshire, inda ya fadawa masu jefa kuri'a cewa a bayan da ya shafe shekaru hudu yana shugabancin Amurka, har yanzu shi ne limamin canji na zahiri a Washington. Daga nan, shugaban yayi tattaki zuwa jihar Florida a kudu, inda ya fadawa magoya baya cewa zai yi aiki tukuru domin karfafa marasa karfi.

Daga nan shugaban ya zarce zuwa Jihar Ohio, kuma da tsakar daren nan ne yake kammala gangaminsa na karshe a yau a Jihar Colorado.

Litinin, jajiberen zabe, Mr. Obama zai sake komawa jihohin Wisconsin da Iowa da kuma Ohio kafin ya koma garinsu Chicago a Jihar Illinois, daga inda zai jira sakamakon zabe daren talata.

Shi kuma Mr. Romney yayi jawabi ga magoya bayansa a jihohin Iowa da Ohio, kafin ya zarce zuwa jihohin Pennsylvania da Virginia. A lokacin da yake gangami a Cleveland dake Jihar Ohio, dan takarar na jam'iyyar Republican yayi alkawarin yin aiki tare da dukkan jam'iyyu idan ya ci zabe.

Litinin, Mr. Romney zai yada zango da safe a Jihar Florida, kafin ya sake komawa jihohin Virginia da Ohio da New Hampshire. Daren talata, Mr. romney zai jira sakamakon zaben a birnin Boston a jiharsa ta Massachusetts.

Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa 'yan takarar guda biyu su na kunnen-doki a muhimman jihohin Colorado da Florida da Ohio da kuma Virginia. Shugaba Obama yana da 'yar rata kadan a jihohin Ohio da Virginia, yayin da Mr. Romney yake da irin wannan 'yar karamar rata a Jihar Colorado.

Wadannan jihohi hudu sune manya a cikin jihohin da har yanzu babu fitaccen gwani, wadanda kuma suke da matukar muhimmanci wajen cimma yawan mazaba 270 da ake bukata kafin dan takara ya zamo shugaban kasa.
XS
SM
MD
LG