Asabar, Agusta 30, 2014 Karfe 06:11

Afirka

Ana Shirin Maida 'Yangudun Hijirar Sudan ta Kudu Zuwa Gida

Wasu 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
Wasu 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
Kabiru Fagge
Rahotanni dake fitowa daga kasar Sudan na cewa hadin gwiwar hukumar kula da rage kwararar ‘yan gudun hijira da kokarta maidasu gida ta MDD (IOM)da hadin kan Gwamnatocin Sudan da Sudan ta kudu sun shirya bullo da wata sabuwar hanyar daukan ‘yan gudun hijirar domin maidasu gida ta jiragen sama.

Shirin zai shafi ‘yan gudun hijirar da yawansu ya kusa kaiwa dubu da dari hudu dake zaune a birnin Khartoum suna jiran tsammani.

An shirya jiragen saman fasinjan dauke da ‘yan gudun hijirar zasu rika tashi ne daga Khartoum zuwa Aweil Arewacin Bahr El-Ghazali Kudancin Sudan.

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio Shirin Safe        MP3

Audio Shirin Rana       MP3

Audio Shirin Dare       MP3

Audio Mu Tattauna       MP3