Talata, Mayu 03, 2016 Karfe 11:35

  Labarai / Afirka

  Sauye-sauye a Dokar Mallakar Filaye a Afirka

  Wata gona a Afirka
  Wata gona a Afirka
  Taron kasa da kasa na masanan kimiyyar bunkasa halin zaman rayuwar al’umma ya maida hankali kan batun samun filayen noma da ginin gidajen jama’a a nahiyar Afirka a zaman muhimmin abin dubawa.
  T
  aron yace rashin karfafa daukan matakan bunkasa harkokin noma a nahiyar Afirka ne ke janyo koma bayan tattalin arziki.Babban taron na kasa da kasa da aka gudanar a kasar Kamaru a ranakin bakwai dfa takwas ga wannan watan  na Nuwamba yayi kiran da a karfafa fannin kimiyyar sanin fannin kimiyyar noma da labarin kasa, a kuma inganta hanyar samar da filaye ga jama’a domin gudanar da ayyukan noma da gioggina gidaje da masana’antu.

  Madiodio Niasse, Darekta na kamfanin ayyukan rarraba filaye a kasar Kamaru, yana muma daga cikin wadanda suka halarci taron ya yi Karin haske.
  A ta bakinsa, “Batun mallakar  fili yanzu ya zama wani babban batun da kasa da kasa ke baiwa muhimmanci, domin an gano cewa batun mallakar fili imma dai na noma ko ginin gida ko kuma masana’antu idan ba’a bi a hankali bas hike zaman ummul haba’isin tada rikici a mafi yawan kasashen Afirka. "

  Darekta Niasse ya kara da cewa, “Yace wani babban dalilin dake janyo hankulan kasa da kasa shine albarkar da kasa ke dashi a fannin noma, ko albarkatun karkashin kasa da kuma jurewa ayyukan masana’antu, shi yasa Afirka ke da martaba a idon duniya.”

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye