Alhamis, Mayu 05, 2016 Karfe 03:50

  Labarai / Sauran Duniya

  Obama ya ci jihar Florida, don haka ya dada tsere ma Romney a adadin kuri'u na karshe

  U.S. President Barack Obama delivers a statement on the U.S. "Fiscal Cliff" in the East Room of the White House, November 9, 2012.
  U.S. President Barack Obama delivers a statement on the U.S. "Fiscal Cliff" in the East Room of the White House, November 9, 2012.
  Ibrahim Garba
  An bayyana Shugaban Amurka Barack Obama a matsayin wanda ya ci zaben jihar Florida inda aka fi yin kare-jini biri-jini, kwanaki hudu bayan da ya sake yin nasara a zaben Shugaban kasa.
   
  Jihar ta Florida da ke kudancin kasar, ita ce kawai jihar da ta kasa kammala kidaya kuri’unta bayan zaben na ranar Talata, wanda Shugaba mai ci dan Democrat da dan Republican Mitt Romney su ka fafata a ciki.
   
  Ofishin harkokin cudanyar na jihar Florida y ace Shugaba Obama ya sami kashi 50% na kuri’un da aka kada a yayin da kuma Romney ya sami kashi 49.1 %, mai nufin tazarar kuri’u 74,000, wanda ya kai adadin da ya wace wanda akan sake kirgawa.
   
  Ko da ma baici jihar da ake wa kirari da “mai hasken rana” tuni ba Shugaba Obama ya sami sama da makin kuri’u 270  da ake bukata kafin zama Shugaban kasa.
   
  A Amurka dai kowace jiha na da adadin makin kuri’u daidai gwargwadon yawan mutanen cikinta, kuma yawan makin na zama daidai da yawan ‘yan Majalisar Dattawanta da na Wakilanta. Duk dan takarar da ya sami kuri’u mafi yawa a jiha, to shi ya ci makin kuri’un jihar, in banda jihohin Maine da Nebraska.
   
  Karin makin kuri’un Florida 29, ya sa adadin makin kuri’un Mr. Obama ya kai 332 na Romney kuma 206.

  Watakila Za A So…

  Sauti Bisa umurnin Buhari an tura kayan tallafi Borno wa 'yan gudun hijira

  Wani kwamiti a karkashin jagorancin babban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya kai Borno wasu kayan tallafi ma 'yan gudun hijira bisa umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari Karin Bayani

  Sauti Daliban makarantar sakandare ta Kano sun rasa rayukansu a hadarin mota

  Dalibai goma sha biyu jihar Kano ta tura zuwa Legas domin gasar ilimin fasaha wanda suka kammala lami lafiya amma akan hanyarsu ta dawowa suka yi hadari tsakanin Legas da Ibadan Karin Bayani

  Sauti FIFA ta girmama marigayi Rashidi Yekini shahararren dan wasan kwallon kafan Najeriya

  Jiya Laraba shahararren dan wasan kwallon kafa na Najeriya Rashidi Yekini ya cika shekaru hudu da rasuwa yana da shekaru arba'in da takwas a duniya. Karin Bayani

  Sauti Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da hukuncin kisa wa masu satar mutane

  Bayan da majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudurin yankewa masu satar mutane hukuncin kisa ita ma majalisar wakilai na gaf da amincewa da kudurin. Karin Bayani

  Kasar India Ta Musanta Zargin Tabarbarewar Addini A Kasar

  Ma’aikatar harkokin wajen India ta ce ba ta yarda da wannan rahoton ba Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye