Talata, Satumba 16, 2014 Karfe 15:26

Sauran Duniya

Yau, 11 ga watan nan na Nuwamba, ta ke Ranar Tunawa da Mazan jiya a nan Amurka

Makabartar Arlington ta kasa
Makabartar Arlington ta kasa
Ibrahim Garba
Yau, 11 ga watan nan na Nuwamba, ta ke Ranar Tunawa da Mazan jiya a nan Amurka, wanda lokaci ne na hutu a kasar baki daya, don karrama dukkannin dakarun da su ka kare Amurka a dukkannin yake-yaken da aka yi.
 
Wannan ita ce ranar tunawa da mazan jiya na farko da ta zo bayan da dakarun Amurka su ka fice daga Iraki cikin watan Disamban bara. Ranar Tunawa da Mazan Jiya ta wannan shekarar kuma wata dama ce ga Amurkawa ta nuna godiya ga baraden yakin duniya na biyu, da yawansu ke ta raguwa sosai.
 
Shugaban Amurka kan ajiye furanni a kowace ranar tunawa da mazan jiya, a kaburburan dakarun da ba a sansu ba, a makabartar tarayya da ke Arlington.

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

        Shirin Safe               0500 - 0530 UTC

Audio Rumbun Shiri        NLive  

        Shirin Hantsi            0700 - 0730 UTC

Audio Rumbun Shiri         NLive  

           0700 - 0730 UTC 

Audio Shirin Rana     Rumbun Shiri   NLive

           1500 - 1530 UTC 

Audio Shirin Dare     Rumbun Shiri   NLive

           2030 - 2100 UTC