Talata, Maris 31, 2015 Karfe 07:38

Najeriya

Aliko Dangote Yafi Kowane Dan Afirka Arziki

Mujallar Forbes ta ce Dangote yana da dukiyar da ta kai ta dala miliyan dubu 12, akasari daga kamfanoninsa na siminti a kasashe 14 na Afirka

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote
Mujallar Forbes ta bayyana wani attajiri dan Najeriya da ya samu kudinsa a fagen sarrafa sukari, fulawa da siminti, a zaman mutumin da ya fi kowane dan Afirka arziki.

Wannan ita ce shekara ta biyu a jere da Aliko Dangote yake zamowa na daya a cikin ‘yan Afirka 40 da suka fi kudi. Mujallar Forbes ta ce Aliko Dangote yana da dukiyar da ta kai dala miliyan dubu 12.

Mujallar Forbes ta ce akasarin kudaden Dangote ya samu ne daga masana’antun yin simintinsa, wadanda suke a cikin kasashe 14 a Afirka.

A bayan Aliko Dangote, akwai wasu ‘yan Najeriya da dama cikin jerin mutanen da suka fi kudi a nahiyar Afirka, cikinsu har da Mike Adenuga wanda shi ne na 5, kuma yana da kimanin dala miliyan dubu 4 da 300; sai Jim Ovia wanda yake lamba ta 17, kuma yana da dukiyar dala miliyan 775; sai Theopilus Danjuma wanda ke lamba ta 21 da dukiyar dala miliyan 600.

Sauran ‘yan Najeriyar sun hada da Oba Otudeko wanda yake lamba ta 24 da dala miliyan 550; da Hakeem Bello Osagie wanda yake lamba ta 28 da dala miliyan 450; sai Abdulsamad Rabiu wanda yake lamba ta 29 da dala miliyan 400; sai kuma Mohammed Indimi dake lamba ta 30 da dala miliyan 330.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: anon Daga: nigeria
11.12.2012 06:41
wanda yafi kowanne dan africa kudi a cikin 'yankasuwa


by: manniru yusuf Daga: jos
07.12.2012 22:55
Dukiyar su bata da amfani ga mutanen Nigeria.Saboda,inda sun zuba jari akasar tare da tallafawa talawa da talauci ya ragu.

Zaben Najeriya a 2015

Muna bukatar hotuna da bidiyon garin ku, ko unguwar ku, da rumfunan zaben ku, da ma duk wani abun da ya shafi zabe tsakanin Jonathan da Buhari. Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

Karin Bayani akan Zaben Najeriya a 2015

Ra’ayoyinku da 2015 Zabe

An soke kuri'u sama da 70,000 a jihar Nassarawa. A tunanin ku me ya janyo haka?

Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

#zaben2015

Muna bukatar hotuna da bidiyon garin ku, ko unguwar ku, da rumfunan zaben ku, da ma duk wani abun da ya shafi zabe tsakanin Jonathan da Buhari. Ku sanar da mu ta Facebook, da Twitter, da Instagram @voahausa sai a kara da wannan shadar ta #zaben2015.

Karin Bayani akan VOA Hausa Facebook