Asabar, Agusta 29, 2015 Karfe 19:51

Labarai / Sauran Duniya

Gobarar Masakar Kasar Bangladesh Ta Hallaka Mutane Sama da 100

Gobarar Masakar Bangladesh
Gobarar Masakar Bangladesh
Ibrahim Garba
‘Yan agaji a Bangladesh na kokarin gano gawarwakin mutane a kalla 112, da akasari mata ne, da gobarar masaka ta rutsa da su.
 
Hukumomi sun ce gobarar ta tashi ne a hawa ta daya ta wani katafaren ginin bene da daren jiya Asabar a bayan Dhaka, babban birnin kasar.
 
‘Yan kwanakwana sun yin awoyi sun a kokarin kashe wutar, a yayin da ma’akata da dama ke makale cikin dukkanin hawa na sama na benen. Wasu daga cikin ma’aikatan sun yi ta dirowa kasa su na mutuwa kafin hukumomi sui so wurin.
 
Jami’ai sun ce bas u san musabbabin wannan gobarar ba kuma wai sun a kan bincike. Shugaban wata kungiyar kare hakkin Ma’aikata a Bangladesh ya gaya wa kamfanin dillanci labaran Faransa cewa wannan gobarar it ace mafi muni a tarihin bangaren masakun kasar.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti