Alhamis, Nuwamba 26, 2015 Karfe 04:16

Labarai / Najeriya

Mutane Akalla 11 Sun Mutu A Tagwayen Hare-Haren Bam

Rundunar sojan Najeriya ta ce wannan bam ya tashi cikin wata majami'a dake wani sansanin soja, ya kashe mutane 11, ya raunata 30.

Mutane sun taru a wani wurin da bam ya tashi kan wata hanya a Kaduna, arewacin Najeriya ran 8 Afrilu, 2012.Mutane sun taru a wani wurin da bam ya tashi kan wata hanya a Kaduna, arewacin Najeriya ran 8 Afrilu, 2012.
x
Mutane sun taru a wani wurin da bam ya tashi kan wata hanya a Kaduna, arewacin Najeriya ran 8 Afrilu, 2012.
Mutane sun taru a wani wurin da bam ya tashi kan wata hanya a Kaduna, arewacin Najeriya ran 8 Afrilu, 2012.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce tagwayen hare-haren bam na kunar-bakin-wake sun ragargaza wata majami'a ta kirista 'yan darikar Protestant lahadi a wani sansanin soja, inda mutane akalla 11 suka mutu, wasu 30 suka ji rauni.

Shugaban matasa na kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Diji Haruna, ya fadawa wakiliyar Muryar Amurka Heather Murdock, cewa an kammala taron ibada a majami'ar a lokacin da bama-baman suka tashi, amma kuma limamai da 'yan kungiyar kwaya na majami'ar su na ciki a lokacin.

Mr. Haruna ya tabbatar da cewa hare-haren sun wakana ne a barikin soja na Jaji, dake Kaduna a arewacin Najeriya.

Wata majiyar soja kuma, ta ce akasarin mutanen da suka mutu, sun rasa rayukansu ne a tashin bam na biyu, a lokacin da suka je taimakawa wadanda suka ji rauni a tashin bam na farko.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma a cikin 'yan watannin baya, kungiyar nan ta Boko Haram ta kai hare-hare kan majami'u a jihar ta Kaduna.

A ranar Jumma'a, rundunar sojojin Najeriya ta gabatar da tayin bayar da tukuicin dubban daloli ga duk wadanda zasu tsegunta mata inda zata kama shugabannin kungiyar Boko Haram. Wata sanarwar rundunar ta bayyana sunayen mutane 19 da ake zargin cewa sui ne manyan wannan kungiya.

Watakila Za A So…

Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shrin Safe

Shrin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: mangal Daga: kano
27.11.2012 06:19
ni agaskiya inagani wadannan mutane sunfi karfin hukuma ko wacce irice du fadan dabaxakaga mutumin da zai cucekaba to inaganin yin sulhu dasu shine a,ala ga nageriya da samun saukinta allah ya bamu zaman lafiya ameen.


by: Yusuf aa haidal p.kwaro don allah masu tada bamabamai kuji tsoron allah kudai don zama lafiya yafi zama dan sarki Daga: daga Bakaro bauchin yakubu
26.11.2012 16:48
Muryar amurka


by: Tijjani Auwalu Daga: Riruwai
26.11.2012 12:39
Daukan rai ya zama ba komai ba ga wasu,to allah ya shirye su.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye