Lahadi, Agusta 30, 2015 Karfe 16:52

Labarai / Afirka

Shugaba Morsi Ya Gana da Alkalan Kasar Masar.

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya gana da majalisar kolin alkalai.

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi tare da sabon babban lauyan gwamnati Talaat AbdullahShugaban kasar Masar Mohammed Morsi tare da sabon babban lauyan gwamnati Talaat Abdullah
x
Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi tare da sabon babban lauyan gwamnati Talaat Abdullah
Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi tare da sabon babban lauyan gwamnati Talaat Abdullah
Halima Djimrao-Kane
Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi zai gana da majalisar kolin alkalan kasar, a daidai lokacin da su ke kokarin shawo kan shugaban kasar su hana shi tarawa kan shi tulin iko a matakin da ya dauka makon jiya.

Dokar ta takalo zanga-zanga daga bangaren ‘yan hamayya, wadanda su ka ci gaba da yin dirshan a dandalin Tahrir a kwana na hudu a jere a yau litinin, su na neman da lallai sai Mr. Morsi ya sake lale, ya sauya shawara.  ‘Yan hamayya da magoya bayan shugaban kasar sun kira tarurrukan gangami daban-daban a birnin a gobe talata.

Dokar da Mr.Morsi ya kafa ta ce duk shawarar da ya yanke ta zauna, ba daukaka kara a kowace kotu kuma ta haramtawa kotunan kasar rusa wani bangaren majalisar dokoki da kuma soke wani daftarin kundin tsarin mulkin da majalisa ke kattabawa. Masu sukan lamiri sun ce Mr.Morsi ya tattarawa kan shi tulin ikon yin kama karya kamar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak wanda boren jama’a ya kora daga mulki.

Shugaban ya ce dokar ta dan wani takadirin lokaci ce  kuma za ta yi aiki har ya zuwa lokacin da za a zabi sabbin ‘yan majalisar dokoki bisa tanadin wani kundin tsarin mulkin da aka yiwa kwaskwarima. Wani kakakin jam’iyar shugaban kasar ta “Freedom and Justice” wadda ke mulki, ya fada a jiya lahadi cewa mai yiwuwa ne dokar za ta yi wata biyu ko kasa da haka, sannan ya bayyana daukan matakin da cewa wani kokari ne na neman tabbatar da dorewar zaman lafiya a kasar Masar.

A nan birnin Washington, D.C, dan majalisar dattaban Amurka mai fada a ji, John McCain ya soki lamirin dokar ta Mr.Morsi wadda ya ce ba za a yarda da ita ba.

Watakila Za A So…

Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shirin Safe

Shirin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.

An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti