Laraba, Fabrairu 10, 2016 Karfe 03:35

  Labarai / Najeriya

  Boko Haram Ta Aikata Cin Zarafin Bil Adama.

  Babbar Lauyar Kotun Duniya mai shigar da kara Fatou Bensouda ta zargi Boko Haram da kisan kai da gallazawa.

  'Yan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Kotun Duniya ke zargi da aikata manyan laifuffukan cin zarafin Bil Adama'Yan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Kotun Duniya ke zargi da aikata manyan laifuffukan cin zarafin Bil Adama
  x
  'Yan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Kotun Duniya ke zargi da aikata manyan laifuffukan cin zarafin Bil Adama
  'Yan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Kotun Duniya ke zargi da aikata manyan laifuffukan cin zarafin Bil Adama
  Halima Djimrao-Kane
  Babbar lauyar kotun duniya mai shigar da kara ta zargi ‘yan tawayen Boko Haram da aikata manyan laifuffukan cin zarafin bil Adama a Najeriya, musamman ma kisan kai da tsangwama.

  Ofishin babbar lauya Fatou Bensouda ya ce akwai kyakkyawar madogarar da ta tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ta tsara wani gagarumin harin gama gari wanda ya yi sanadiyar mutuwar Kiristoci da Musulmi fiye da dubu daya da dari biyu daga wajejen tsakiyar shekarar dubu biyu da tara.

  Rahoton, wanda aka kwarmatawa kafofin yada labarai, ya bukaci hukumomin Najeriya da su gurfanar da wadannan manyan laifuffuka a gaban kotu, in ba haka ba, kotun duniya za ta iya daukan matakin yin hakan ita da kan ta.

  Game kuma da zarge-zargen cewa cibiyoyin jami’an tsaron Najeriya su ma, su na aikata laifuffukan cin zarafin bil Adama, rahoton  ya ce  babu wata alamar da ta nuna cewa, wadannan abubuwan da ake zargin su da aikatawa na daga cikin wata manufar gwamnati ko tsarin da aka shirya takanas da sunan cin mutuncin fararen hula.

  A watan jiya, kungiyar kare hakkokin bil Adama ta Human Rights Watch, ta ce daga shekarar dubu biyu da tara fadan da ake yi tsakanin Boko Haram da gwamnatin Najeriya ya lankwame rayukan mutane fiye da dubu biyu da dari takwas, daga cikin su kamar dubu daya da dari uku sun mutu ne sanadiyar irin matakan da jami’an tsaron Najeriya ke dauka.

  Watakila Za A So…

  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

  An rufe wannan dandalin
  Yadda Ake Son Gani
  Sharhi/Ra'ayi
       
  by: Kabiru sani Daga: kano
  01.12.2012 06:24
  To mudai Fatan mu Allah yabamu zaman lafiya a wanan kasa tamu

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye