Asabar, Mayu 23, 2015 Karfe 14:22

Afirka

Mayakan M23 Sun Ce Za Su Bar Goma Amma Da Sharadi

'Yan tawayen Kwango sun yi alkawarin ficewa daga Goma idan sun samu biyan bukata daga gwamnatin kasar

'Yan tawayen M23 su na yin sintriri a garin Goma'Yan tawayen M23 su na yin sintriri a garin Goma
x
'Yan tawayen M23 su na yin sintriri a garin Goma
'Yan tawayen M23 su na yin sintriri a garin Goma
Halima Djimrao-Kane
Shugaban sashen harakokin siyasar kungiyar ‘yan tawayen Congo ta M23 ya ce dakaraun shi za su gaggauta ficewa daga garin Goma da suka kama idan sun samu biyan bukata daga gwamnati.

Jean-Marie Runiga ya yi wannan furuci ne a yau talata a Goma a lokacin da ya ke magana da manema labarai. A makon jiya ‘yan tawayen su ka kama garin na Goma a gabashin kasar kuma tun daga wannan lokaci su ka kama garin Sake a yammacin kasar.

Darektan sashen harakokin wajen kungiyar M23, Rene Abandi ya fadawa Muryar Amurka da safiyar talata cewa shugaban bangaren sojojin kungiyar ya yi alkawarin cewa askarawan shi za su bar Goma nan da nan bayan wata ganawa da hafsoshin sojojin Uganda da Rwanda da na Jamahuriyar Demokradiyar Congo.

Abandi ya ce ba a dauki wannan mataki saboda wani matsin lamba ba, amma an yi ne don a nuna kyakkyawar niyar ‘yan tawayen ta tattaunawa da gwamnati.

Shugabannin kasashen yankin, a cikin su har da shugaban kasar Jamahuriyar Demokradiyar Congo Joseph Kabila sun bukaci da lallai sai M23 ta fice daga Goma da faduwar ranar litinin.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti