Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Binne Sauran Gawar Marigayi Yasser Arafat


Jami'an tsaron Falasdinawa na gadin kushewar marigayi Yasser Arafat a Ramallah, Yammacin Kogin Jordan
Jami'an tsaron Falasdinawa na gadin kushewar marigayi Yasser Arafat a Ramallah, Yammacin Kogin Jordan

Kwararrun kasa da kasa sun tono sauran gawar marigayi Arafat don su yi bincike a kan musabbabin mutuwar shi mai cike da al'ajabi da daure kai

Jami’an gwamnatin Falasdinawa sun ce kwararrun masanan kasa da kasa sun sake mayar da sauran gawar marigayi Yasser Arafat kabari sun binne bayan sun tono ta don su yi karin bincike game da musabbabin mutuwar shi.

Jami’ai sun ce da jijjifin talata masanan su ka tono sauran gawar Arafat daga katafaren hubbaren da ta ke ciki a birnin Ramallah a yammacin kogin Jordan.
An mika samfurin abun da aka cira daga gawar ga kwararrun masanan kasar Faransa da Switzerland da Russia da kuma Falasdinawa, wadanda su kuma za su koma kasashen su na asali su gudanar da bincike a kai.

A farkon shekarar nan ta dubu biyu da goma sha biyu jami’an gwamnatin kasar Faransa su ka bayar da umarnin cewa a gudanar da bincike akan mutuwar Yasser Arafat bayan an ga burbushin munmunar gubar maganad’isun nukiliya ta polonium mai kisa a jikin tufafin Arafat da aka karba a wurin matar shi.

Nan da nan gubar polonium ke rozayewa, kuma wasu kwararru sun ce babu tabbas ko za a iya samun isasshen samfurin da za a yi gwaji a kai.
Yasser Arafat ya rasu a shekarar dubu biyu da hudu a kasar Faransa jim kadan bayan ya kamu da wata irin cuta mai daure kai.

A kasashen Larabawa an dage a kan shaci fadin cewa Israila ce ta ba shi guba, amma Israila ta musanta zargin.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG