Lahadi, Mayu 01, 2016 Karfe 10:53

  Labarai / Afirka

  'Yan Tawayen M23 Na Shirin Ficewa Daga Birnin Goma

  'Yan tawayen Congo na shirin fita daga Goma amma ba wata alamar da ta nuna za su yi wata gagarumar janyewa daga yankin

  'Yan tawayen kasar Congo na sintiri a wani titin garin Sake a tazarar kilomita 25 arewa da birnin Goma'Yan tawayen kasar Congo na sintiri a wani titin garin Sake a tazarar kilomita 25 arewa da birnin Goma
  x
  'Yan tawayen kasar Congo na sintiri a wani titin garin Sake a tazarar kilomita 25 arewa da birnin Goma
  'Yan tawayen kasar Congo na sintiri a wani titin garin Sake a tazarar kilomita 25 arewa da birnin Goma
  Halima Djimrao-Kane
  ‘Yan tawayen Jamahuriyar Demokradiyar Congo sun shirya ficewa daga birnin Goma na gabashin kasar a yau Jumma’a, amma nan take babu wasu alamu da ke nuna wata gagarumar janyewa daga birnin.

  Kungiyar ‘yan tawayen M23 ta ce za ta janye zuwa wani sansani a tazarar kilomita 20 a bayan garin babban birnin lardin mai tarin muhimmanci, amma za su bar sauran sojoji kimanin 100 a filin jirgin saman birnin na Goma.

  Kungiyar ‘yan tawayen wadda, ta kama birnin Goma a makon jiya bayan ta fafata da sojojin Congo da na Majalisar Dinkin Duniya masu tsaron zaman lafiya, ta yi amai ta lashe game da alkawarin ta na ficewa daga birnin ranar alhamis bisa yarjejeniyar da aka cimma da shiga tsakanin sauran kasashen yankin.

  Kungiyar ta fara tattara nata ya nata ta na ficewa daga sauran yankunan gabashin kasar Jamahuriyar Demokradiyar Congo, amma wakilin Muryar Amurka Gabe Jaselow ya ce ‘yan tawaye da yawa sun kwashi ganima a gidajen mutane a garin Sake, a ranakun laraba da alhamis a lokacin da su ke ficewa daga yankin.

  Mutanen da rikicin kasar Congo ya kora daga gidajen suMutanen da rikicin kasar Congo ya kora daga gidajen su
  x
  Mutanen da rikicin kasar Congo ya kora daga gidajen su
  Mutanen da rikicin kasar Congo ya kora daga gidajen su


  Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Congo ya shaidawa Muryar Amurka cewa sun tabbatar an aikata abubuwan keta haddin bil Adama a birnin Goma.

  Ranar laraba gwamnatin kasar Jamahuriyar Demokradiyar Congo ta zargi kungiyar ‘yan tawayen M23 da kisan mutum 64 a garin Goma da kuma raunata fararen hula fiye da 220. Ranar alhamis kungiyar M23 ta gabatar da sanarwar musanta zargin.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye