Litinin, Agusta 31, 2015 Karfe 03:31

Labarai / Sauran Duniya

Israila Za Ta Rike Wasu Kudaden Falasdinawa

Israila ta ce za ta rike kudaden Falasdinu sama da dola miliyan 100 don ladabtar da ita saboda nasarar da ta yi a Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban kasar Falasdinu Mahmoud Abbas a Ramallah, ya na gaida mutanen da su ka yi cincirindo su na murnar samun matsayin KasaShugaban kasar Falasdinu Mahmoud Abbas a Ramallah, ya na gaida mutanen da su ka yi cincirindo su na murnar samun matsayin Kasa
x
Shugaban kasar Falasdinu Mahmoud Abbas a Ramallah, ya na gaida mutanen da su ka yi cincirindo su na murnar samun matsayin Kasa
Shugaban kasar Falasdinu Mahmoud Abbas a Ramallah, ya na gaida mutanen da su ka yi cincirindo su na murnar samun matsayin Kasa
Halima Djimrao-Kane
Israila ta ce a wani matakin ladabtar da Falasdinawa saboda nasarar da suka yi a Majalisar Dinkin Duniya za ta rike wasu kudaden su sama da dola miliyan dari da ta tattara mu su a haraji da kudin fito.

Israila ta dauki wannan mataki ne a yau lahadi a daidai lokacin da Falasdinawa su ka yi cincirindo cikin murna su ka tarbi shugaba Mahmoud Abbas a birnin Ramallah na yammacin kogin Jordan bayan nasarar diflomasiyar da ya yi a makon jiya lokacin da Falasdinu ta samu matsayin kasa ‘yar kallon da ba ta da kujera a babban taron MDD.

A lokacin da ya ke yin jawabi ga ‘yan tarbon shi, Mr. Abbas ya furta cewa: << yanzu mu na da kasar mu>>.

Ministan kudin Israila Yuval Steinitz ya fada a yau lahadi cewa gwamnatin su za ta yi amfani da kudaden da ya kamata su baiwa Falasdinawa, su biya bashin da kamfanin wutar lantarkin Israila ke bin Falasdinu, da kuma sauran wasu kamfanoni.

Haka kuma a yau lahadi, bai daya gwamnatin Israila ta zartas da kudirin yin watsi da matakin Majalisar Dinkin Duniya na baiwa Falasdinu matsayin kasa.  Gwamnatin Israila ta ce ba za ta tattauna game da yammacin kogin Jordan, da Gabashin birnin Kudus da kuma Zirin Gaza bisa dogaro da matakin da babban taron Majalisar ya dauka ya amince da Falasdinu a matsayin kasa ba.

Wannan ne matakin ramuwar gayya na biyu da Israila ta dauka. Ranar Jumma’a ma Israila ta yi sanarwar cewa za ta gina dubban gidajen ‘yan kaka gida a yankunan Falasdinu na yammacin kogin Jordan.

Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da kuri’ar amincewa da sabon matsayin Falasdinun ne cikin tsananin adawar Israila da Amurka.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti