Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 11:16

Najeriya

An Kai Hari Kan Wani Kauye A Jihar Borno

Wasu mutanen da ake zaton ‘yan kishin Islama ne sunkai farmaki kauyen Chibok a Jihar Borno, suka kashe mutane akalla 10 mabiya addinin kirista.

Sojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar BornoSojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar Borno
x
Sojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar Borno
Sojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar Borno
Wasu mutanen da ake kyautata zaton ‘yan kishin Islama ne sun fantsama a wani kauyen dake arewacin Najeriya suka kashe mutane akalla 10 mabiya addinin kirista.

Mazauna kauyen Chibok a Jihar Borno sun ce ‘yan bindiga sun kutsa cikin kauyen ran asabar da daddare suka kai farmaki kan kiristocin. Shaidu sun ce wadannan mahara sun yanka mutanen suka kuma kona gidajensu.

Har yanzu jami’an gwamnatin Najeriya ba su tabbatar da bayanin wannan harin ba, amma wani jami’i yace watakila aikin kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun dora ma kungiyar Boko Haram alhakin mutuwar mutane fiye da dubu 3 tun shekarar 2009 a lokacin da ta yi yunkurin kafa tafarkin Islama a arewacin Najeriya. Wuraren da ta ke kai wa hari sun hada da ofisoshin ‘yan sanda da majami’u.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Lauwali bala masama Daga: Masama bukkuyum local govt zamfara
25.12.2012 07:45
Allah yakawo Maiduguri zaman lafiya amin

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti