Lahadi, Fabrairu 14, 2016 Karfe 13:35

  Labarai / Afirka

  An Bankado Shirin Neman Kaiwa Jam'iyar ANC Hari

  'Yan sandan kasar Afirka ta Kudu sun kama wasu mutane hudu masu tsattsauran ra'ayi bisa zargin shirya makarkashiyar kai hari kan babban taron ANC

  Shugaba Jacob Zuma na rera waka ranar bude babban taron jam'iyar ANC a Bloemfontein, a kasar Afirka ta Kudu.
  Shugaba Jacob Zuma na rera waka ranar bude babban taron jam'iyar ANC a Bloemfontein, a kasar Afirka ta Kudu.
  Halima Djimrao-Kane
  ‘Yan sandan kasar Afirka ta Kudu sun kama wasu masu tsattsauran ra’ayi hudu wadanda ake zargi da shirya makarkashiyar kai hari a lokacin da jam’iyar da ke mulkin kasar ke gudanar da babban taron ta.

  A yau litinin hukumar ‘yan sandan kasar ta bayar da sanarwar kama mutanen , amma ba ta yi cikakken bayani ba, ta ce ranar lahadi aka kama mutanen ‘yan shekaru 40 zuwa 50.
  Jam’iyar ANC ce ke rike da mulkin kasar Afirka ta Kudu tun shekarar 1994 da aka kawo karshen mulkin turawan kasar ‘yan tsiraru, kuma ta na yin babban taron ta na kwanaki biyar a birnin Bloemfontein.

  Kakakin ANC, Keith Khoza, ya fada a yau litinin cewa har yanzu jam’iyar na jiran cikakken rahoto a kan kama mutanen, kuma ya ce makarkashiyar kai harin wani al’amari ne mai tayar da hankali. Ya ce barazanar da ake yi saboda launin fata, abu ne mai ban tsoro, amma ya ce jam’iyar ANC za ta ci gaba da yin babban taron ta cikin gagarumin tsaro.

  Ya ce sun damu saboda har yanzu a cikin su akwai wasu daidaikun mutanen da ke da irin wannan tunani. Ya ce hakan ya na nufin cewa ana fuskantar babban kalubale. Ya ce kasar Afirka ta Kudu ta ga abu mafi muni, kuma ya ce ba sa fatan sake komawa cikin yanayin tashin hankali saboda launin fata ko ta’addanci. Ya ce hakan bai dace da abun da  ‘yan kasar Afirka ta Kudu baki dayan su ke kokarin cimma ba.
     
  Jam’iyar Federal Freedom ta gwagwarmayar kwatar ‘yancin turawan Afrikaner ‘yan tsiraru, ta bayar da sanarwar cewa biyu daga cikin wadanda aka kama mambobin ta, amma ta nisanta kan ta da duk wata makarkashiyar shirya kai hari.

  Watakila Za A So…

  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye