Laraba, Mayu 04, 2016 Karfe 20:16

  Labarai / Sauran Duniya

  Dalibar Da Aka Yi Ma Fyade A Indiya Ta Mutu

  'Yan sanda sun damke mutane 6 da ake tuhuma, kuma bayan tuhumar fyade, a yanzu zasu fuskanci tuhumar kisan kai da yake dalibar ta rasu

  Indiyawa da suka taru su na addu'a ma dalibar da wasu mutane suka taru suka yi mata fyade, wadda ta rasu yau asabar
  Indiyawa da suka taru su na addu'a ma dalibar da wasu mutane suka taru suka yi mata fyade, wadda ta rasu yau asabar
  Wata dalibar kasar Indiya wadda wasu mutane suka taru suka yi mata fyaden taron dangi a wannan wata cikin wata motar safa a New Delhi, ta rasu yau asabar da asuba a wani asibitin kasar Singapore.

  Wata sanarwar da asibitin Mount Elizabeth ya bayar, ta ce wannan mace mai shekaru 23 da haihuwa ta rasu cikin "kwanciyar hankali" da asuba.

  Firayim minista Manmohan Singh na Indiya yace yayi matukar bakin cikin mutuwar wannan matashiya. Yace kowa yana iya fahimtar irin fusatar da al’ummar kasar Indiya ke nunawa kan lamarin wannan daliba.

  A yau asabar aka shirya za a mayar da gawarta zuwa kasar Indiya.

  An fuskanci zanga-zanga da gangamin dubban jama’a a birnin New Delhi tun ranar da aka kai ma wannan mace farmaki. Jami’ai a birnin New Delhi sun ce su na damarar ganin karin zanga-zanga a bayan mutuwarta yau asabar.

  An ce wannan mace tana tafiya tare da wani abokinta namiji cikin wata motar safa ranar 16 ga watan Disamba a New Delhi sai wasu mazaje su 6 dake cikin motar suka ciro rodi na karfe suka lakkada musu duka da ita da wannan aboki nata. Daga nan suka yi ta yi mata fyade. Daga nan kuma sai suka jefa ta waje daga cikin motar tare da shi abokin nata.

  ‘Yan sanda sun damke mutanen shida da ake zargi da wannan danyen aiki, kuma an tuhume su da fyade. Yanzu kuma su na fuskantar laifin kisan kai a bayan mutuwarta.

  Watakila Za A So…

  Kasar India Ta Musanta Zargin Tabarbarewar Addini A Kasar

  Ma’aikatar harkokin wajen India ta ce ba ta yarda da wannan rahoton ba Karin Bayani

  ‘Yan Sandan Faransa Sun Yi Amfani Da Barkonon Tsohuwar Akan Masu Zanga-Zanga

  Akalla ‘yan gudun hijira 150 ne suka mamaye makarantar Jean Jaures Karin Bayani

  Afrika Zata Gudanarda Taron Kan Shirin Dashen Itatuwa

  Tun shekarar 2005 aka fidda shawarar shirin da ake kira da turanci "Great Green Wall" Karin Bayani

  Donald Trump Yace Nasarar Da Ya Samu Gagaruma Ce

  Donald Trump bukaci hadin kan 'ya'yan jam’iyyar Republican Karin Bayani

  Sauti Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun Ta Ceto Tsohuwar Ministan Ilimi

  Babu tabbacin cewa an biya kudin fansa ga wadanda suka yi garkuwa da wannan tsohuwar Minista Karin Bayani

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye