Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 00:33

  Labarai / Sauran Duniya

  Obama Ya Yi Alwashin Shawo Kan Mallakar Bindiga

  Shugaba Obama ya yi alkawarin yin matsin lambar gaggauta samar da sabbin matakan shawo kan mallakar bindigogi a Amurka

  Bindigogi a Majalisar Dokokin jahar Oklahoma
  Bindigogi a Majalisar Dokokin jahar Oklahoma
  Halima Djimrao-Kane
  Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi alkawarin bada cikakken goyon bayan fadar White House ga kokarin neman shan kan rigimar bindiga a nan Amurka. 
  Mr.Obama ya fada ranar lahadi, a cikin wata tattaunawa da gidan talbijin din NBC a shirin “Meet the Press” cewa harin da aka kai kwanakin baya kan wata makarantar elemantare a jahar Connecticut wanda ya halaka yara ishirin da manya shida, ita ce rana mafi muni a cikin shekaru hudun da ya yi ya na shugabanci.

  Shugaban ya ce zai bukaci goyon bayan Amurkawa game da shawarwarin tsananta binciken halin masu neman sayen bindigogi, da haramta sayar da makaman yaki da kuma zungurun harsashai masu karfin tsiya. Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ne zai jagoranci ayarin masu tsara dokar da za ta kawo karshen harbin gama gari a Amurka inda ‘yancin mallakar bindiga ke rubuce a cikin kundin tsarin mulki.

  Mr.Obama ya ce sabbin matakan shan kan mallakar bindigogi za su janyo cacar baki, amma dole ne Amurka ta duba ta gani ko ta na da karfin halin daukan sabbin matakan yiwa hancin tufka, maimakon ta bari a manta da harin da aka kai kan makaranta. Shugaba Barack Obama ya ci gaba da bayani ya na cewa: “Kenan tambayar da za mu yi ita ce, a hakikanin gaskiya shin ko mun yi kaduwar da ta isa ta hana mu mantawa da abun da ya faru, kamar irin abubuwan da su ka saba faruwa a yi kwana da kwanaki ana magana a kai, kuma a yi watsi da abun a bar maganar. Ba shakka ni dai ba haka na ke jib a. Wannan wani abu ne wanda, ka na ji, ita ce rana mafi muni a shugabanci na. Kuma ba na fata Allah Ya maimaita”.

  Amma Mr.Obama ya ce ya na tababa game da kiran da babbar kungiyar kare muradun wadanda su ka mallaki bindigogi a Amurka ta yi cewa a saka masu gadi da bindigogi a duka makarantun gwamnatin da ke cikin kasar Amurka su kusan dubu dari. Mr. Obama ya ci gaba da bayani ya na cewa: “Ina tababar cewa hanya daya ta tinkarar wannan ita ce ta kara saka bindigogi a makarantu. Kuma a tunani na mafi yawan Amurkawa na tababar cewa wannan ita ce hanyar da za ta warware ma na matsalar mu”.

  A wani batu na daban kuma shugaban ya ce akwai wasu manyan matsaloli game da tabbatar da tsaro a ofisoshin jakadanci wadanda su ne su ka zama sanadin kisan da aka yiwa jami’an jakadancin Amurka hudu a Benghazi ranar goma sha daya ga watan satumba. Ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a kan harin, amma ya ki amsa tambayar neman sanin wadanda jami’an gwamnatin Amurka su ka dorawa laifin kai harin.

  Watakila Za A So…

  Sauti Najeriya Ba Zata Kara Kashe Kudi Ba Don Nemawa Jami’anta Magani A Kasar Waje

  Duk da yake kowanne dan kasa na da ‘yancin fita domin neman waraka daga cutar dake damunsa, babban abin takaici inji shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, a ta bakin ministan lafiya, shine yadda yan kasar ke yin tururuwa a kasashen waje domin neman maganin rashin lafiya. Karin Bayani

  Sauti An Baiwa Babban Akanta Janar Na Jihar Bauchi Wa’adi Ya Biya Albashi

  Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta baiwa babban akanta janar na jihar wa’adin mako guda daya biya dukkan ma’aikatan jihar da aka kammala aikin tantancesu albashi. Karin Bayani

  Sauti Anya Kuwa Rundunar Zaman Lafiya Dole Sun San Inda Aka Ajiye Yan Matan Chibok?

  Cikin watan Maris ne a cibiyar yaki da Boko Haram dake Maiduguri, kwamandan rudunar Zaman Lafiya Dole, Manjo Janar Leo Irabor, ya bayar da kwarin gwiwar karya lagon ‘yan ta’adda da nuna cewa za a kawo karshensu nan bada dadewa ba. Karin Bayani

  Sauti Boko Haram Na Shigar Da Makamansu Najeriya Ta Boyayyun Hanyoyi

  Tsohon hafsan rundunar sojan saman Najeriya, Aliko El-Rashid Harun, wanda kwararre ne kan sha’anin tsaro yace akan shigo da makamai ga yan Boko Haram cikin Najeriya ta kan iyakokin kasar, wanda ke da yawan gaske kuma ba a saka musu idanu. Karin Bayani

  Sauti Ra’ayoyin Yan Jihar Kaduna Game Da Wasu Dokoki A Jihar

  Wasu daga cikin yan jihar Kaduna da shugabannin al’umma na ci gaba da korafe korafe game da wasu daga cikin dokokin da gwamna mallam Nasiru El-Rufa’in jihar Kaduna yakai gaban Majalisa. Karin Bayani

  Sauti An Kai Hari A Garin Egrak A Jamhuriyar Nijar

  Wandansu mutane da ba a san ko suwaye ba sun kai hari a yammacin jiya, a wani kauye da ake kira Egrak, dake cikin jihar Tawa a kasar jamhuriyar NIjar. Karin Bayani

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye