Qazi Hussain Ahmed Na kasar Pakistan Ya Rasu
Babban masanin addinin Islama kuma shugaban jam'iyar Jamaat-e-Islami Qazi Hussain Ahmed ya rasu ranar lahadi a Islamabad ya na da shekara 74
Jana'izar tsohon shugaban jam'iyar Jamaat-e-Islami, Qazi Hussain Ahmed wanda ya rasu a Islamad ranar lahadi ya na da shekara 74
Halima Djimrao-Kane
07.01.2013
WASHINGTON, DC — Babban masanin addinin Islama dan kasar Pakistan, Qazi Hussain Ahmed, ya rasu ya na da shekaru saba'in da hudu.
Shi ne tsohon shugaban babbar jam’iyar addinin kasar Pakistan ta Jamaat-e-Islami, shekaru ishirin da biyu ya yi, ya na shugabantar ta kafin ya yi murabus a shekarar dubu biyu da tara.
A watan nuwamban da ya gabata, Ahmed ya tsallake rijiya da baya, ya tsira ba ko kwarzane daga wani yunkurin neman yi mi shi kisan gilla lokacin da wani dan harin kunar bakin wake ya fasa boma-bomai daf da shi.
Ya na daya daga cikin manyan masu sukan lamirin yakin hadin guiwar Amurka da kungiyar kawancen tsaro ta NATO su ke yi a makwafciyar kasar Afghanistan.
Qazi Hussain Ahmed ya rasu da safiyar lahadi a Islamabad. Da ma shekara da shekarru ya na fama da cutar zuciya.
Marigayi Qazi Hussain Ahmed, tsohon shugaban jam'iyar Jamaat-e-Islami ta kasar Pakistanx
Marigayi Qazi Hussain Ahmed, tsohon shugaban jam'iyar Jamaat-e-Islami ta kasar Pakistan