Asabar, Nuwamba 28, 2015 Karfe 06:50

Labarai / Sauran Duniya

An Rage Hukumcin Da Za A Iya Yankewa Kan Manning

Mai shari’a ta rage hukumcin da za a iya yankewa a kan sojan Amurka da ake tuhuma da satar mika bayanan sirri na Amurka ga kungiyar Wikileaks.

Firabiti Bradley Manning, a tsakiya, yana fitowa daga motar jami'an tsaro zai shiga kotu a Fort Meade, Jihar MarylandFirabiti Bradley Manning, a tsakiya, yana fitowa daga motar jami'an tsaro zai shiga kotu a Fort Meade, Jihar Maryland
x
Firabiti Bradley Manning, a tsakiya, yana fitowa daga motar jami'an tsaro zai shiga kotu a Fort Meade, Jihar Maryland
Firabiti Bradley Manning, a tsakiya, yana fitowa daga motar jami'an tsaro zai shiga kotu a Fort Meade, Jihar Maryland
Wata mai shari’a ta soja a nan Amurka ta rage irin hukumcin da za a iya yankewa a kan wani sojan Amurka da ake tuhuma da laifin satar mika bayanan sirri na Amurka ga kungiyar nan ta Wikileaks.

Jiya talata mai shari’a Denise Lind ta yanke hukumcin cewa zata rage kwanaki 112 a kan duk wani hukumcin da za a iya yankewa a kan Bradley Manning a saboda yadda aka tozarta masa a wani kurkukun soja bayan kama shi.

Ana tsare da Manning tun tsakiyar shekarar 2010. A wasu lokutan, hukumomi sun killace shi shi kadai cikin dakin da ko taga babu na tsawon sa’o’I 23 kowace rana, wani lokacin ma tsirara.

Mai shari’ar ta yanke hukumci a lokacin zaman sauraron shaida kafin fara shari’ar cewa wasu daga cikin abubuwan da aka yi masa sun wuce kima, ko da gwamnati tana da damuwa ta zahiri kan wasu abubuwan. Amma kuma ta ce irin wannan musgunawa da aka yi masa ba ta kai ta yadda zata biya bukatun lauyoyi masu kare shi cewa a kori karar ba.

Manning yana fuskantar tuhume-tuhume 22, ciki harda “taimakawa abokan gaba” wanda hukumcinsa yana iya kaiwa daurin rai da rai. Za a fara shari’arsa a ranar 6 ga watan Maris.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye