Jumma’a, Mayu 06, 2016 Karfe 04:29

  Labarai / Afirka

  Faransa Na Shirin Taimaka Wa Mali

  Dakarun Ansar Dine a zaune akan mota a garin Gao dake arewa maso gabashin Mali. June 18, 2012. Dakarun Ansar Dine a zaune akan mota a garin Gao dake arewa maso gabashin Mali. June 18, 2012.
  x
  Dakarun Ansar Dine a zaune akan mota a garin Gao dake arewa maso gabashin Mali. June 18, 2012.
  Dakarun Ansar Dine a zaune akan mota a garin Gao dake arewa maso gabashin Mali. June 18, 2012.
  Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande yace a shirye kasarsa ta ke ta dakile kutsen da ‘yan tawaye masu tsatsaurar ra’ayin Islama ke yi a Mali, to amman zai yi hakan ne kawai da amincewar Majalisar Dinkin Duniya.
   
  Mr. Hollande ya fadi a wani jawabin daya yi yau Juma’a cewa kutsen wata tsabar barazana ce ga kasancewar Mali. Ya kara da cewa Faransa za ta ji rokon Mali na neman taimako bisa sharadin da Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya Shinfida.
   
  A jiya Alhamis ne Kwamitin Tsaron yayi wani zama na tattaunawa kan rikicin na Mali, bayan da ‘yan tawaye su ka kama wani muhimmin gari a yunkurin da suke yi zuwa babban birnin kasar ta Kudu. Kwamitin ya bayar da umurnin tura sojojin kasashen waje cikin gaggawa don su dakile wannan matsalar.
   
  Shugaban wuccin gadin Mali Dioncounda Traore ya roki Faransa, wadda ita ta yi wa Mali mulkin mallaka, da ta taimaka masu cikin gaggawa don dakile ‘yan tawayen.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye