Laraba, Mayu 04, 2016 Karfe 16:26

  Labarai / Afirka

  Faransa Ta Kai Hari Ta Sama Kan 'Yan Tawayen Mali

  Sojojin Najeriya da na Senegal ma su na can kasar ta Mali domin dafawa sojojin gwamnati a kokarin murkushe 'yan kishin Islama da suka doshi kudu

  Mayakan kungiyar Ansar Dine zaune a mota a garin Gao, arewa maso gabashin Mali, ran 18 Yuni, 2012.
  Mayakan kungiyar Ansar Dine zaune a mota a garin Gao, arewa maso gabashin Mali, ran 18 Yuni, 2012.
  Jiragen saman yaki na Faransa sun kai hare-hare a kasar Mali domin tallafawa sojojin gwamnati dake kokarin jan burki ma wasu mayaka ‘yan kishin Islama da suka doshi kudu.

  Jiya jumma’a, ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya tabbatar da kai hare-haren ta sama, amma ya ki bayarda karin haske game da wadannan matakan sojan.

  Tun farko a jiya jumma’ar, Faransa ta ce ta aika da sojojinta zuwa Mali a bisa rokon gwamnatin kasar. Har ila yau, an tura sojoji daga Najeriya da Senegal zuwa Mali domin dafawa sojojin gwamnati.

  Jami’an sojan Mali sun ce harin da aka kai ta saman ya ja burki ma ‘yan kishin Islamar. ‘Yan tawayen dake rike da dukkan arewacin Mali, sun kutsa kudu a wannan mako, suka kama garin Konna. Jami’an sojan Mali sun ce a yanzu dakarun gwamnati sun sake kwato garin.

  Jiya jumma’a, shugaban rikon kwarya na Mali, Dioncounda Traore, ya ayyana dokar ta baci a kasar, ya kuma yi kira ga kowane dan kasar Mali da ya taimaka a wannan yaki.

  Shugaba Francois Hollande na Faransa, yace sojojin Faransa su na taimakawa wajen yakar abinda ya kira gungun ‘yan ta’adda a kasar Mali.

  Shugaban kasar Mali dai ya roki Faransa, wadda ta yi ma kasar mulkin mallaka, da ta kai musu daukin gaggawa don dakile farmakin ‘yan tawayen. Majiyoyin diflomasiyya sun ce Mr. Traore zai gana da shugaba Hollande a Paris ranar laraba mai zuwa.

  Sakataren harkokin wajen Britaniya, William Hague, ya fada jiya jumma’a cewa Britaniya tana goyon bayan shawarar da Faransa ta dauka ta tsoma hannun sojojinta a rikicin Mali.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye