Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Kasashen Dake Makwabtaka Da Kasar Mali Sun Fara Isa Mali


Motar yaki a birnin Bamako dake Mali
Motar yaki a birnin Bamako dake Mali
Sojin kasashen dake Makwabtaka da kasar Mali sun fara isa Mali yau lahadi domin tallafawa sojin Faransa a rana ta uku kokarta kakkabe barazanar da mayakan ‘yan tawaye ke yiwa yankin Arewacin Mali.

Tun jiya Asabar kasashen Nijer, da Burkina Faso da Senegal suka bada sanarwar tura sojinsu, kwana guda bayan da sojin faransa suka fara kaiwa ‘yan tawayen hari ta jiragen saman yaki.


Anji Jami’an Faransa a yau lahadi na fadin cewa sojin Faransa na samun nasarar maida mayakan ‘yan tawayen zuwa baya daga garin Konna ta amfani da hare-haren jiragen saman yaki da kuma karfafa kai kora daga sojin kasa.

Nasarar da mayakan ‘yan tawayen suka samu wajen kame wani garin dake Arewa maso gabashin Bamako, babban birnin kasar Mali ya baiwa ‘yan tawayen sukunin iya kaiwa ga kame birnin Mopti dake Arewaci, birnin da ke hannun kulwar sojin Gwamnatin Mali.

Kafar labarai a Mali ta shaidawa wakilin Muryar Amurka cewar an kashe da yawa daga cikin mayakan ‘yan tawaye a gwabzawar da aka yi domin kubutar da garin na Konna, kuma sojin kasar Mali tun daga daren jiya Asabar suka sami sukunin sake kutsawa domin kame garin bayan da mayakan ‘yan tawayen suka rika ja da baya. Har yanzu garuruwan Bore da Douentza na hannun ‘yan tawayen.
XS
SM
MD
LG