Talata, Disamba 01, 2015 Karfe 15:37

Labarai / Sauran Duniya

'Yan Sandan Isra'ila Sun Fatattaki Falasdinawa

Runudnar ‘yan sandan Isra’ila tayi amfani da karfi wajen korar Falasdinawan dake zanga-zanga a yankin Falasdinawan da Isra’ila ta mamaye yanzu take kokarin gigginawa Yahudawan kama wuri zauna gidaje a Yammacin Kogin Jordan.

Mazaunar Isra'ilawa kennan dake Maaleh Adumim. Dec. 2. 2012Mazaunar Isra'ilawa kennan dake Maaleh Adumim. Dec. 2. 2012
x
Mazaunar Isra'ilawa kennan dake Maaleh Adumim. Dec. 2. 2012
Mazaunar Isra'ilawa kennan dake Maaleh Adumim. Dec. 2. 2012
Runudnar ‘yan sandan Isra’ila tayi amfani da karfi wajen korar Falasdinawan dake zanga-zanga a yankin Falasdinawan da Isra’ila ta mamaye yanzu take kokarin gigginawa Yahudawan kama wuri zauna gidaje a Yammacin Kogin Jordan.
 
‘Yan kishin kasar Falasdinu sun kokarta kakkafa tantuna a yankunan nasu da ake kira da lakabin E-1 ran Juma’a, suka ce suna karfafa cewar yin haka ne zai sa Isra’ila ta tsaida gine-ginen da take yi yanzu a Yammacin Kogin Jordan.

Falasdinawa sun yi watsi da gargadin da sojin Isra’ila suka yi masu na su janye, don haka yau lahadi safe sai ‘yan sandan Isra’ila cikin motocin rusa gine-gine suka bulla a yankin inda suka rika bi suna rurrusa tantunan ‘yan falasdinu.

Yahudawan kama wuri zauna a Isra’ila sun jima dama suna shiga yankunan Falasdinawa suna giggina gidaje tare da ikrarin ai yankin na daga cikin wuraren da Isra’ila  ta mamaye a Yammacin Kogin Jordan.

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye