Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 18:46

  Labarai / Afirka

  Tankokin Yakin Faransa Sun Doshi Bakin Daga A Mali

  Wakiliyar Muryar Amurka ta ce tankoki da sojojin na Faransa su na kan hanyar zuwa arewacin kasar dake hannun 'yan tawaye masu kishin Islama.

  Sojojin Faransa cikin motoci masu sulke sun doshi arewa daga Bamako, babban birnin kasar Mali, Talata 15 Janairu 2013
  Sojojin Faransa cikin motoci masu sulke sun doshi arewa daga Bamako, babban birnin kasar Mali, Talata 15 Janairu 2013
  Jerin gwanon tankokin yaki na Faransa, sun bar Bamako, babban birnin kasar Mali a jiya talata, suka doshi arewacin kasar dake hannun ‘yan kishin Islama.

  Wakiliyar Muryar Amurka, Anne Look, ta ce a bisa dukkan alamu tankokin sun doshi inda sojojin Faransa suka ja daga ne. Faransa tana kara yawan dakarunta a kasar Mali, inda ta aike da tankoki da motocin yaki masu sulke, yayin da take ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan tawaye daga sama.

  Look ta ce a jiya talata, motocin yaki guda 100 na Faransa sun isa Mali daga Ivory Coast makwabciyarta, kuma karin sojoji sun doshi can daga Chadi da Faransa.

  A halin da ake ciki, shaidu sun ce jiragen yakin Faransa sun yi luguden wuta a kan garin Diabaly cikin dare, ‘yan sa’o’i kadan a bayan da mayaka masu nkishin Islama suka kama wannan gari mai tazarar kilomita 400 a arewa da birnin Bamako. Mazauna garin sun ce har yanzu ‘yan tawayen ne ke rike da garin.

  Jami’an tsaro na Faransa sun ce sannu kan hankali, yawan dakarunsu a Mali zai karu zuwa dubu 2 da 500. Najeriya kuma ta ce a yau laraba sojojinta na farko zasu sauka a kasar Mali, a wani bangare na rundunar sojojin kasashen Afirka ta Yamma da zasu taimaka ma sojojin gwamnatin Mali wajen kwato arewacin kasar.

  Shugaba Francois Hollande na Faransa ya fada jiya talata a Dubai cewa sojojin faransa zasu zauna a Mali har sai an samu kwanciyar hankali.

  Tsagera masu alaka da kungiyar al-Qa’ida sun kwace arewacin Mali a bayan da wasu bijirarrun sojoji suka hambarar da gwamnatin kasar a watan Maris, suka haddasa yanayi na rashin hukuma na wani dan lokaci a kasar.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye