Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 02:26

  Labarai / Afirka

  Kungiyar Al-Shabab Ta Yanke Shawarar Kashe Dan Faransa

  Hoton dan Faransa kennan wanda ake kira Dennis Allex a hoton da shafin al-Shabab ya wallafa ran Yuli 9 2010 Hoton dan Faransa kennan wanda ake kira Dennis Allex a hoton da shafin al-Shabab ya wallafa ran Yuli 9 2010
  x
  Hoton dan Faransa kennan wanda ake kira Dennis Allex a hoton da shafin al-Shabab ya wallafa ran Yuli 9 2010
  Hoton dan Faransa kennan wanda ake kira Dennis Allex a hoton da shafin al-Shabab ya wallafa ran Yuli 9 2010
  Kungiyar ‘yan gwagwarmayar Somaliya al-Shabab tace ta shirya daukan matakin kashe dan Faransa da suke garkuwa da shi ‘yan kwanaki kadan bayan kokarin da Faransa tayi na kokarin ceto shi amma bata sami nasara ba. Bayan ta kasa cin nasara sai Faransa ta dauka mutumin ya mutu.
   
  A wata sanarwa  ranar Laraba ‘yan gwagwamayar sun ce sun cimma shawarar baki daya su kashe dan leken asirin Faransa Denis Allex.

  Ana tsare Allex tun lokacin da aka sace shi daga birnin Mogadishu daga wani otel a watan Yuli a shekarar 2009. Kafin lokacin yana cikin ayarin dake horar da dakarun gwamnatin Somali domin yakar al-Shabab.
   
  Dakarun Faransa sun yi kokarin kubutar da Allex a wani samame da suka kai ranar Juma’a lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sojojin Faransa biyu da mayakan al-Shabab 17
   
  Al-Shabab tace fararen hula dakarun Faransa suka kashe lokacin samamen. Kungiyar tace zata kashe Allex domin daukan fansar wadanda suka mutu kuma ta nuna rashin amincewarta da abun da ta kira manufofin Faransa da suka nuna kin jinin Islama da kuma shigar da dakarun Faransa suka yi cikin Afghanistan da Mali.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye