Jumma’a, Mayu 06, 2016 Karfe 19:43

  Labarai / Sauran Duniya

  An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Hedkwatar 'Yan Sandan Leken Asiri A Afghanistan

  Jami’an Afghanistan sun ce ma’aikatan tsaro biyu sun rasa rayukansu sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai wa hedkwatar ‘yan sandan leken asiri ta kasar a birnin Kabul.

  'Yan Afghanistan kennan suna saka wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a cikin mota a Kabul, January 16, 2013.'Yan Afghanistan kennan suna saka wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a cikin mota a Kabul, January 16, 2013.
  x
  'Yan Afghanistan kennan suna saka wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a cikin mota a Kabul, January 16, 2013.
  'Yan Afghanistan kennan suna saka wadanda harin kunar bakin wake ya shafa a cikin mota a Kabul, January 16, 2013.
  Jami’an Afghanistan sun ce ma’aikatan tsaro biyu sun rasa rayukansu sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai wa hedkwatar ‘yan sandan leken asiri ta kasar a birnin Kabul.
   
  ‘Yan sandan Afghanistan sun fada cewa wata mota cike da bama-bamai ta tarwatse a dai-dai kofar shiga hedkwatar hukumar tsaro ko kuma “National Directotare of Security” da rana yau Laraba.

  Tarwatsewar ta haddasa mugun hayakin da ya turnuke sararin samaniya. Har wala yau an kashe wasu mahara biyar dauke da nakiyoyi yayin da suke fitowa daga mota ta biyu suna kokarin kutsawa cikin hedkwatar.

  ‘Yan sanda sun ce mota ta biyun ita ma cike take da nakiyoyi amma sun samu sun warwaresu.

  Ita dai hedkwatar ‘yan sandan leken asirin kasar tana kusa da wasu gine-ginen gwamnati ne a birnin na Kabul wadanda suka hada da ma’aikatar tsaron cikin gida.

  Jami’ai sun ce kusan mutane 30 ne suka samu raunuka a harin wanda ya tarwatsa gilashi da karafa ya baza su kusa da wasu shaguna.Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin a sakon da ta aika ta wayar tafi da gidanka.

  Watakila Za A So…

  Sauti Ana Gina Masallacin Da Yafi Kowanne Girma A Duniya

  Rahotanni daga kasar Algeria na cewa kasar zata gina katafaren masallacin da ba irin sa a duniya a wajen girma, domin ya zame wa kungiyoyin Musulmi masu matsanci ra’ayi wani babban kalubale. Karin Bayani

  Sauti Najeriya Ta Sami Guraban Matasa 100 a Shirin YALI

  Kimanin matasa yan Najeriya su 100 ne a bana suka sami damar zuwa kasar Amurka a shirin nan na mandela washington fellow, YALI, shirin da shugaba Obama ya kirkiro don Horas Da Matasa Manyan Gobe na Afirka, yana dora matasa kan turbar ci gaba ta hanyar ilmantarwa, horaswa kan shugabanci da kuma mu'amala. Karin Bayani

  Sauti Boko Haram: Mutane Na Murnar Komawa Gidajensu

  Yayin da gwamnatin APC a Najeriya ke cika shekara guda a karagar mulki, rahotanni na nuni da cewa al'amurra sun fara komawa a wuraren da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram, yayin da mutane ke ci gaba da komawa gidajensu. Karin Bayani

  Sauti Kura Ta Lafa Bayan Rikicin Kabilanci a Aba

  Raohatanni daga Najeriya na cewa hankula sun fara kwanciya bayan tashin hankalin da ya auku jiya tsakanin ‘yan Arewacin Najeriya da ke gudanar harkokin kasuwanci a birnin Aba na jihar Abia, da kuma ‘yan kabilar Igbo. Karin Bayani

  Harin Syria kan sansanin yan gudun hijira ya kashe mutane 30

  Sa'o'i kadan bayan jami'an Rasha da Syria sun tabbatar da tsagaita wuta a birnin Aleppo sai jiragen yaki na Syria ko Rasha suka soma ruwan bamabamai kimanin kilimita 30 daga birnin lamarin da ya kaiga hasarar rayuka 30 Karin Bayani

  Sauti Yar'adua Shugaba Ne Na Hakika - Jonathan

  Shekaru shida ke nan da Allah ya yiwa tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Yar'adua rasuwa, rasuwar da ta kaiga mataimakinsa Goodluck Jonathan daga yankin Niger Delta ya dare kan mulki Karin Bayani

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye