Talata, Mayu 03, 2016 Karfe 04:00

  Labarai / Afirka

  Sojojin Algeria Sun Kai Farmaki Akan Mayakan Sa Kai A Kamfanin Iskar Gas

  Kamfanin Iskar Gas inda mayaka ke garkuwa da mutane. Photo Credit. AFP PHOTO/STATOIL/KJETIL ALSVIKKamfanin Iskar Gas inda mayaka ke garkuwa da mutane. Photo Credit. AFP PHOTO/STATOIL/KJETIL ALSVIK
  x
  Kamfanin Iskar Gas inda mayaka ke garkuwa da mutane. Photo Credit. AFP PHOTO/STATOIL/KJETIL ALSVIK
  Kamfanin Iskar Gas inda mayaka ke garkuwa da mutane. Photo Credit. AFP PHOTO/STATOIL/KJETIL ALSVIK
  Sojojin Algeria sun kai wani farmaki a kan harabar kamfanin iskar Gas, inda mayakan sa kai masu alaka da al-Qaida suke garkuwa da mutane da suka kama jiya laraba.
   
  Wani mai magana da yawun ‘yan mayakan yace an kashe akalla mutane 34 cikin wadanda ake garkuwa da  su, da kuma ‘yan fashin su 15. 
   
  Babu wani cikakken bayani kan harin na yau. Kamfanin dillancin labarai na kasar Mauritania yace ya sami jimlar wadanda farmakin na yau ya rutsa da su  ne daga daya daga cikin mayakan sakai dake harabar kamfanin.
  Kamfanin dillancin labarai na kasar Aljeriya ya bada labarin cewa jiragen sama masu saukar ungulu su kai hari yayinda mayakan ke kokarin fita daga kamfanin tare da wasu daga cikin mutanen da suka kama. Mayakin da yayi magana da yawun ‘yan fashin, wanda bai bayyana ko shi waye ba, ya gaya wa kamfanin dillacin labaran cewa a kalla turawa guda 7 ne da ake garkuwa da su ke raye.
   
  Ta wani gefen kuma, kamfanin dillacin labarai na Algeria, yace sojoji sun kwaci wasu ‘yan kasashen waje daga hannun mayaka. Rahotannin farko sun ce wadanda ake kwata da dan Kenya, ‘yan kasar Faransa guda biyu, da biyu daga Birtania.
   
   
  Mayakan sakai masu kishin Islama  wadanda suke da alaka da kungiyar al-Qaida sun bada labarin kama kimanin mutane 41 ‘yan kasashen ketare akamfanin jiya Laraba, mataki da mayakan suka ce ramuwar gayya ce kan matakin soja da Faransa ta dauka a makwabciyar kasar, watau Mali.
   
  Wani kakakin kungiyar al-Qaida a yankin Maghreb reshenta dake Mali, ya gayawa Muryar Amurka cewa akwai Amurkawa cikin wdanda ake garkuwa da su. Jami’an Amurka sun gaskanta cewa akwai Amurkawa cikin wadanda ake garkuwa  da su.
   
  Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta ya kira garkuwa  da mutanen a matsayin ta’addanci.
   
  Sauran mutanen da hannun mayaka sun hada da ‘yan kasashen Britaniya, Faransa, Japan, Norway da  kuma Ireland.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye