Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 14:57

  Labarai / Afirka

  Mazuna Wani Gari Da Mayakan Sa Kai Suka Kama Sun Fara Gudu A Mali

  Jirgin sama mai saukar ungulu na Faransa a tashar jirgin sama na birnin Bamako dake Mali. Junairu 16, 2013.Jirgin sama mai saukar ungulu na Faransa a tashar jirgin sama na birnin Bamako dake Mali. Junairu 16, 2013.
  x
  Jirgin sama mai saukar ungulu na Faransa a tashar jirgin sama na birnin Bamako dake Mali. Junairu 16, 2013.
  Jirgin sama mai saukar ungulu na Faransa a tashar jirgin sama na birnin Bamako dake Mali. Junairu 16, 2013.
   A Mali mazauna wani gari da mayakan sakai suka kama a farkon makon nan sun fara gudu, yayinda wadansu kuma suka bada labarin ana gwabza fada tsakanin mayakan sakai da  sojojin Faransa a wajajen gefen yankin.
   
  Wani dan jarida a yankin ya gaywa wakiliyar Muriyar Amurka Anne Look cewa ya ga mutane masun yawa suna barin Diabaly a yau Alhamis, sun doshi kudanci daga arewacin kasar da ahalin yanzu yake hanun ‘yan tawaye. Ya  ce woyoyin tarho a garin sun daina aiki, kuma zauna garin sun bada labarin mayakan sakai sun girke a sassan daban daban na garin.

  Ahalinda ake ciki kuma, ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, yace dakarun kasar 1,400 sun isa Mali. Kasar ta ayyana tura dakaru 2, 500 wadanda za su ci gaba da zama kasar har sai kome ya daidaita.

  Manyan hafsoshin kasashe dake yammacin Afirka sun ce sojoji daga Najeriya, Nijar, Cadi, da Burkina Faso, da kuma Togo su 2,000 nan bada jumawa ba zasu fara isa Mali daga yau Alhamis, a matsayin wani rukuni da sojoji da Majalisar dinkin duniya ta bada umarnin a tura su domin shawo Kan rikicin kasar.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye