Talata, Maris 31, 2015 Karfe 21:44

Afirka

Kungiyar Al-Shabaab Ta Kashe Dan Kasar Faransa

Hoton jami'in leken asirin dan kasar Faransa, Dennis Allex wanda al-Shabaab tace ta kashe. Oktoba. 4, 2012Hoton jami'in leken asirin dan kasar Faransa, Dennis Allex wanda al-Shabaab tace ta kashe. Oktoba. 4, 2012
x
Hoton jami'in leken asirin dan kasar Faransa, Dennis Allex wanda al-Shabaab tace ta kashe. Oktoba. 4, 2012
Hoton jami'in leken asirin dan kasar Faransa, Dennis Allex wanda al-Shabaab tace ta kashe. Oktoba. 4, 2012
Kungiyar mayakan sakai al-Shebab dake Somalia ta bada labarin cewa ta kashe dan kasar Faransan nan da take garkuwa da shi fiye da shekaru uku.

A wani labari da ta saka a dandalin Twitter yau Alhamis, kungiyar tace tun jiya laraba ta kashe bafarnshen mai suna Denis Allex.

Jiya laraba al-shabab ta bada sanarwar niyyarta na kashe jami’in leken asiri na Faransan, wanda yunkurin da Faransa tayi na ceto shi cikin makon jiya ya faskara. Dama tuni jami’an kasar ta Faransa suka aza cewa jam’in da ake garkuwa da shi ya mutu.

Al-shabab tace ta dauki matakin ne domin abunda ta kira kashe farar hula da dakarun Faransa suka yi lokacin da suka kai somamen nema kubutar da jam’in kasar ranar jumma’a da ta shige, da kuma bayyana rashin amincewarta kan manufofin muzgunawa musulmi da Faransa take dauka, da kuma matakan sojin kasar a Faransa da kuma Afghanistan.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti