Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Jarida A Somalia


'Yan jarida a gidan radion Shabelle na tattauna hare-haren da ake kaiwa 'yan jarida a baya-bayannan.
'Yan jarida a gidan radion Shabelle na tattauna hare-haren da ake kaiwa 'yan jarida a baya-bayannan.
Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani dan jarida har lahira wnda yake aiki da wata kafar yada labarai mai zaman kanta a Mogadishu babbab birnin kasar, Somalia.

Kafar yada labaran ta Shaballe ta fadi cewa an harbi dan jaridar mai suna Abdihard Osman Adan sau dayawa lokacin da ya ke kan hanyar zuwa wurin aiki da sanyin safiyar yau jumma’a.

Shi dai wannan dan jaridar shine na farko da aka kasha a cikin wannan sabuwar shekarar ta 2013 a Somalia, kasar data fi kowace kasa muni ga yan jarida a Afirka. Kusan ‘yan jarida 20 ne aka kasha a kasar a shekarar da ta gabata.

Kafar yada labarum Shaballe, wadda aka kase mata ‘yan jarida da yawa a yan shekarun nan, ta bayyana Adan a matsayin dan jarida mai kwazo sosai.

Kafar yada labaran tayi kira ga hukumomin da su dauki matakan tsaro akan wuraren aikin yan jaridar, domin su samu zarfin gudanar da ayyukansu ba tare da shiga cikin wani hadari ba.
XS
SM
MD
LG