Lahadi, Maris 29, 2015 Karfe 20:31

Sauran Duniya

Majalisar Dinkin Duniya Bata Cimma Yarjejeniya Ba Da Iran Akan Nukiliya

Hoton Herman Nackaerts kennan, na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya. Junairu 15, 2013.Hoton Herman Nackaerts kennan, na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya. Junairu 15, 2013.
x
Hoton Herman Nackaerts kennan, na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya. Junairu 15, 2013.
Hoton Herman Nackaerts kennan, na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya. Junairu 15, 2013.
Shugaban spetocin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce ba’a cimma wata yarjejeniya da kasar Iran akan binciken shirin nukiliyarta wanda ya jawo cece kuce ba. Amma yace, a watan gobe idan Allah ya kaimu za a yi wani taro akan wannan batu.

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ko kuma IAEA a takaice, Herman Nackaerts ya fada a yau Jumma’a cewa, shi da tawagarsa sun isa filin saukar jiragen Vienna bayan ganawar kwanaki biyu a Tehran babban birnin kasar Iran.

Yayin da yake bayyana bambamcin dake tsakaninsu da kasar Iran din, Nackaerts ya ce bangarorin biyu basu iya cimma matsaya daya ba kan yadda za’a warware matsalolin ba. Ya ce zasu sake tattaunawa ranar 12 ga watan gobe, idan Allah ya kaimu.

Hukumar ta IAEA ta yi zaton, samun sukunin shiga sansanin soja a Parchin, wurin da ke kasashen yammacin turai ke na da alaka da kera makaman nukiliya. Iran ta dage akan cewa wurin, sansani ne na soja kawai, kuma shirinta na nukiliya, tana yi ne a saboda bukatun samun zaman lafiya.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti