Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Na Sa Ran Mutane 700,000 Ne Zasu Kauracewa Mali


Hoton Zeinab Mint Hama, 25, da yaranta Zuber (hagu), Bon Oumar (na biyu a hagu) and Seydna Ali a sansanin 'yan gudun hijira mai Mbera refugee camp a kudancin Mauritania, May 23, 2012.
Hoton Zeinab Mint Hama, 25, da yaranta Zuber (hagu), Bon Oumar (na biyu a hagu) and Seydna Ali a sansanin 'yan gudun hijira mai Mbera refugee camp a kudancin Mauritania, May 23, 2012.
Hukumar lura da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace tana sa ran cewa mutane dubu dari bakwai ne zasu kaurace wa gidajensu a Mali a saboda fadanda ake fafatawa tsakanin yan tawayen Musulmi da dakarun kasa-da-kasa da ke mara wa sojojin Mali baya.

Rikicin da ake yi a Mali ya riga ya raba fiye da mutane dubu dari ukku da hamsin da mahalinsu a cikin shekarar da ta gabata.

Yau jumma’a hukumar ta fada cewa fadan zai iya yin sanadiyar karin mutane 300,000 su rasa matsuguninsu, ya kuma kara sa mutane 400,000 yin gudun hijira zuwa kasashe makwabtan Mali.

Mai magana da yawun hukumar lura da 'yan gudun hijira, Helene Caux ta fadawa muryar Amurka cewa hukumar na samun ruhotanni dake cewa za'a sami kwararuwar yan gudun hijra.

A halin da ake ciki kuma, Sojojin Mali sunce, sun kwace ikon birnin Konna, yayainda dakarun Faransa da na yankin suke cigaba da kwararawa zuwa kasar don yaki da yan tawayen.

Rundunar Sojin Mali ta ce ta samu cikakken iko akan birnin bayan da ta fatattaki yan tawaye da ke wurin. A makon jiya ‘yan yakin sa kai suka mamaye birnin, al’amarin daya sa Faransa ta shigo cikin lamarin kasar, kasar data taba yi wa mulkin mallaka.

Sojojin Mali sun bada ruhoton nasarorin da suka samu a Konna, amma babu cikkaken bayani akan lamarin, saboda yan jarida sun sami matsalar shiga birnin.

Farmakin mayar da murtani da dakarun Faransa da na kasashen Afrika ta yamma su kayi na mako guda, za'a ce ya dakatarda kutsawar da mayakan masu alaka da al-Qaida ke yi, amma duk da haka sun fuskanci turjewa sosai fiye da yadda suke zato.
XS
SM
MD
LG