Litinin, Maris 02, 2015 Karfe 20:00

Najeriya

An Kai Wa Sarkin Kano Farmaki

Hoton jami'an tsaro kennan daura da gidan Gwamna a Kano, Nigeria. (Isiyaku Ahmed/VOA)Hoton jami'an tsaro kennan daura da gidan Gwamna a Kano, Nigeria. (Isiyaku Ahmed/VOA)
x
Hoton jami'an tsaro kennan daura da gidan Gwamna a Kano, Nigeria. (Isiyaku Ahmed/VOA)
Hoton jami'an tsaro kennan daura da gidan Gwamna a Kano, Nigeria. (Isiyaku Ahmed/VOA)
Wadansu da ba'a san ko su waye ba, sun kai wa jerin gwanon motocin Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero hari, a lokacin da yake kan hanyarshi ta zuwa gida daga bikin saukar Qur'ani a Masallacin Murtala dake karamar hukumar Kumbotso yau Asabar.

Wakilin Muryar Amurka daga jihar Kano dake arewacin Najeria, Muhammad Salisu Rabi'u, ya bada rahoton cewa sarkin mai shekaru 82, na cikin motarsa ne akan titin Hausawa dake kusa Zoo Road, a birnin Kano a lokacin da aka bude wa ayarin motocin nasa wuta.

Rahoton yace wasu dake tare da Sarkin sun rasa rayukansu, sannan da yawa sun jikkata a ciki harda jami'an gwamnati.

Ba'a san takamai-mai ba ko wani abu ya samu Alhaji Ado Bayero, wanda yayi shekaru 49 akan karagar mulki. Sai dai kuma har gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kai wa sarkin ziyara domin jajanta masa dangane da wannan hari.

Jami'an tsaro da rundunar dakarun hadin gwiwa ta Najeria, wato Joint Task Force basu ce komai akan wannan farmaki, kuma mutanen garin na ta jimami. 

Birnin Kano wadda aka sani da hada-hadar kasuwanci na cigaba da rayuwa kamar yau da kullum, sai dai akwai jami'an tsaro a wurare da dama.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti