Asabar, Maris 28, 2015 Karfe 17:00

Sauran Duniya

Yanzu Ake Bikin Rantsar Da Barack Obama Na Wa'adi Na Biyu

Majalisar Dokokin Amurka kennan a safiyar da ake bukin rantsar da shugaban kasa, Litinin, Junairu. 21, 2013 (AP Photo/Scott Andrews, Pool)Majalisar Dokokin Amurka kennan a safiyar da ake bukin rantsar da shugaban kasa, Litinin, Junairu. 21, 2013 (AP Photo/Scott Andrews, Pool)
x
Majalisar Dokokin Amurka kennan a safiyar da ake bukin rantsar da shugaban kasa, Litinin, Junairu. 21, 2013 (AP Photo/Scott Andrews, Pool)
Majalisar Dokokin Amurka kennan a safiyar da ake bukin rantsar da shugaban kasa, Litinin, Junairu. 21, 2013 (AP Photo/Scott Andrews, Pool)
Yau litinin za’a kara rantsar da shugaban Amurka Barack Obama a bikin rantsarwa da za’a yi a gaban jama’a a bakin harabar yammacin majalisar dokokin Amurka, a inda zai yi jawabi, kafin ya taka zuwa fadar shugaban kasa ta White House domin fara wa’adinsa na biyu akan karagar mulki.
 
Mutane wajen dubu dari takwas ne ake tsammanin zasu hallara a farfajiyar da ake kira National Mall, dake gaban ginin Majalisar dokokin Amurka. Wannan kiyasi dai ya gaza na bikin rantsar da Obaman a wa’adinsa na farko a inda kusan mutane miliyan biyu ne suka bayanna domin gani an rantsar da shugaban kasa na farko mai launin bakar fata.
 
A hukumance, Mr. Obama ya riga ya dauki rantsuwar kama bakin aiki jiya lahadi saboda kundun tsarin mulkin Amurka ya sharrada da’a ranstar da shugaban kasa ran 20 ga watan junairu. Babban alkali mai shari’a John Roberts ne ya jagoranci rantsarwar, kamar yadda yayi wa shugaban a shekara ta 2009.
 
Bikin rantsar da shugaban kasa na yau ya zone rana daya da ran tunawa da haihuwar Mr. King.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti