Talata, Satumba 16, 2014 Karfe 17:27

Afirka

Sojoji Da Tankokin Yaki Sun Zagaye Ma'akatar Gwamnati A Eritrea

Hoton yankin kasar EritreaHoton yankin kasar Eritrea
x
Hoton yankin kasar Eritrea
Hoton yankin kasar Eritrea
Rahotanni dake fitowa daga babban birnin Eritrea, Asmara, sunce sojoji da tankokin yaki sun zagaye ma’akatar yada labarai bayan da sojojin masu tawaye suka kwace ginin.
 
Rahotannin sunce kimamin sojoji 100 ne suka kutsa ma ma’aikatar yau litinin, kuma suka tilastawa ma’aikatan gidan  talabijin karanta wata sanarwar dake bukatar a saki dukkan fursunonin siyasa.

A wata sanarwar, ofishin jakadancin Britania a Eritrea yace ya samu rahotanni dake cewa akwai sufurin soji na ba saban ba, a birnin Asmara, kuma ofishin ya kara da cewa akwai alamun an rufe gidajen radio da talabijin na birnin.
 
Shugaban Eritrea, Isaias Afeworki yana gudanar da mulkin kama karya a kasar  tun lokacinda ta samu ‘yan cin kai daga Ethiopia a shekara ta 1993.

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

        Shirin Safe                 0500 - 0530 UTC

Audio       Rumbun Shiri                       Live 

        Shirin Hantsi            0700 - 0730 UTC

Audio       Rumbun Shiri                       Live  

        Shirin Rana                1500 - 1530 UTC

Audio        Rumbun Shiri                      Live  

        Shirin Dare                2030 - 2100 UTC

Audio        Rumbun Shiri                      Live