Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 09:09

Afirka

Tsohon Shugaban Liberia Charles Taylor Ya Daukaka Kara

Hoton tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a gidan alkali a kasar Saliyo. Junairu 22, 2013.Hoton tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a gidan alkali a kasar Saliyo. Junairu 22, 2013.
x
Hoton tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a gidan alkali a kasar Saliyo. Junairu 22, 2013.
Hoton tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a gidan alkali a kasar Saliyo. Junairu 22, 2013.
Tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da kotun kasa da kasa ta yankewa hukuncin daurin shekaru hamsin a kurkuku kan aikata laifukan ta’addanci, kisan kai da yiwa mata fyade tare da cusa kananan yara ayyukan soja a lokacin yakin basasar kasar Saliyo yanzu ya daukaka kara.
 
Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta musamman dake bin bahasin laifukan yakin da aka tafka a rikicin kasar Saliyo, wadda kuma ke zamanta a birnin Hague, yau talata ta fara sauraren daukaka karar ta Charles Taylor.

Anji Lauyoyin Charles Taylor na yin kira ga kotun daukaka karar da ta share hukuncin da kotun farko ta yanke tare da rage karfin hukuncin domin yayi tsanani.

Amma lauyoyin gabatar da mai laifi gaban shari’a sun dage kan sai kotun ta bar hukuncin farko domin laifukan da Charles Taylor ya aikata sun wuce gaban mai hankali.

Idan dai za’a tuna, a watan Afrilun shekarar 2012 ne kotun farko ta yankewa Charles Taylor hukuncin daurin bayan da ta sameshi da laifuka har goma sha daya na wulakanta mutuncin Bil Adama tare da goyon bayan mayakan ‘yan tawayen Saliyo da samar masu tulin makamai.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti