Alhamis, Mayu 05, 2016 Karfe 13:20

  Labarai / Najeriya

  Gwamnatin Jihar Kano Ta Hana Daukar Mutane Akan Babur

  Hoton cikin birnin Kano kennan. Hoton cikin birnin Kano kennan.
  x
  Hoton cikin birnin Kano kennan.
  Hoton cikin birnin Kano kennan.
  Gwamnatin jihar Kano ta hana daukar mutane akan babur daga ran Alhamis, 24 ga wannan wata a cikin birnin Kano, da kananan hukumomin kewaye.

  A jawabin da mataimakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi Talatan nan, dan Jam'iyyar Peoples Democratic Party yace hakan zai taimaka wajen yi wa bubura rejista da kuma takalar rashin tsaro dake damun birnin Kano.

  Wakilin Muryar Amurka, Muhammad Salisu Rabi'u ya bada rahoton korafin da Kungiyar 'Yan Achaba na jihar Kano keyi na rashin ayyukanyi, da kuma rashin cika alkawari da gwamnatin jihar Kano tayi musu. 

  Shugaban Kungiyar 'Yan Achaba na jihar Kano, Alhaji Muhammad Sani Hassan ya gayawa wakilinmu cewa gwamnatin ta sanar dasu akan wannan batu, kuma ta shafa wa idannunta kwalli, na cewa ba'a yarda akai yara makaranta ba, ko mara lafiya asibiti akan babur. Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar tayi wa 'yan achaba alkawarin motocin bus dari biyu domin sana'a tun watan Yuni, amma zuwa yanzu, guda ishirin kawai aka basu. Ya kira gwamnati da ta sake duban wannan doka.

  Sana'ar achaba dai, na daya daga cikin hanyoyin samun kudi a Najeria, amma jihohi da dama sun hana yin ta. A jihar Kano, Hukumar Kudaden Shiga na Cikin Gida ta ce tayi rejistan 'yan achaba guda miliyan daya da dubu dari takwas. Wannan kiyasi dai bai hada da mutanen dake amfani da baburansu ba, domin harkokin yau da kullum.

  Wakilinmu, Muhammad Salisu Rabi'u ya gana da mutane a cikin gari domin jin yadda suka karbi wannan mataki. Wani dan achaba, mai suna Muhammad Yusuf yace babban kalubalen da yake fuskanta yanzu, shine samun aikin yi.

  Sana'ar achaba a jihar Kano dai, anyi shekaru 30 ana yi amma a baya-bayannan, 'yan bindiga da bata gari na amfani da ita domin kai hare-hare, fashi, ko sufurin makamai a Najeria.

  Ga mutane da yawa wadanda basu da halin mallakar mota, babur shine abu mafi sauki da suke amfani dashi domin sufurin iyalansu, da sauran harkokin rayuwa.

  Wannan sanarwa dai ta zo ne kwana uku bayan da aka kaiwa sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero farmaki, a lokacin da yake kan hanyarshi ta zuwa gida daga saukar Qur'ani a cikin birnin Kano. A wannan hari, mutane shida ne suka rasa rayukansu, wasu kuma sun jikkata.

  A halin da ake ciki dai, Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso baya gari a lokacin da wakilinmu ya neme shi domin jin karin bayani.

  Watakila Za A So…

  Gwamnan Ohio ya janye daga neman takarar shugabancin Amurka

  Gwamnan jihar Ohio John Kasich ya janye daga takarar neman Shugabancin Amurka jiya Laraba, ya bar abokin hamayyarsa Biloniyan nan mai harkar gidaje kuma tauraron Talbijin Donald Trump, wanda ake hasashen zai zama dan takarar Republican. Karin Bayani

  Wani Alkalin kotun Amurka na iya kiran Clinton ta bayyana a kotunsa

  Wani alkalin kotun tarayya a Amurka yace, akwai yiwuwar ya bada umarnin Hillary Clinton ta bayyana a gaban kotu game da bada ba’asin amfani da hanyar sakon email na kashin kanta wajen aiwatar da aikin gwamnati a lokacin da take sakatariyar wajen Amurka. Karin Bayani

  Muguwar gobarar daji ta kusa lakume garin Fort McMurray a kasar Canada

  Daukacin jama’ar birnin Fort McMurray da ke Alberta a kasar Canada sun kauracewa birnin sakamakon yaduwar wutar daji mafi muni da aka taba gani a yan shekarun nan. Karin Bayani

  Mr. Mulenga Sata tsohon ministan Zambia ya canza sheka zuwa jam'iyyar adawa

  Tsohon ministan yankin Lusaka babban birnin kasar Zambia Mulenga Sata na jam’iyyar Patriotic Front mai mulki ya canza sheka zuwa babbar jam’iyyar kasar UPND a gabanin zaben kasar mai zuwa a watan Agustan bana. Karin Bayani

  Amurka da Rasha sun sake cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Aleppo dake Syria

  Amurka da Rasha sun cimma wata karamar yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Aleppo na kasar Syria, inda mummunan fadan da ake yi tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye ya kashe fiye da farar hula 280 daga watan Afirilu. Karin Bayani

  Sanata Abdullahi Adamu ya musanta batun an ba 'yan majalisa kudaden ayyuka a mazabunsu

  Sanata Abdullahi Adamu shugaban kwamitin dake kula da harkokin noma ya karyata batun cewa an basu kudaden ayyukan mazabunsu Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye