Asabar, Afrilu 30, 2016 Karfe 06:14

  Labarai / Afirka

  Watakila A Kara Yawan Sojojin Afirka A Mali

  Jerin gwanon motocin yakin Faransa a kan wata a wajen garin Markala dake Mali. Junairu 22, 2013. Jerin gwanon motocin yakin Faransa a kan wata a wajen garin Markala dake Mali. Junairu 22, 2013.
  x
  Jerin gwanon motocin yakin Faransa a kan wata a wajen garin Markala dake Mali. Junairu 22, 2013.
  Jerin gwanon motocin yakin Faransa a kan wata a wajen garin Markala dake Mali. Junairu 22, 2013.
  Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce sai tayu a rubanya yawan sojojin Afirka da ake girkewa a Mali su dubu uku da dari uku, domin ana bukatar karin sojoji da zasu taimaka wajen kwato arewacin kasar, wadda ahalin yanzu mayakan sakai masu ikirarin musulinci suke rike da shi.

  Jakadan Ivory Coast a Majalisar Dinkin Duniya Yusuf Bamba, wanda har ila yau shine wakilin ECOWAS  a majalisar, ya ce tuni kamar sojoji dubu daya daga yankin sun isa Mali. A jiya talata ya sake kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta samarda gudumawar kudi na gaggawa da kuma wasu kayan aiki domin taimakawa matakin sojin da aka dauka.

  Dakarun faransa da na Mali sun takawa mayakan sakan birki, wadanda suka fara dannowa ta kudancin kasar, bayanda suka kama kusan arewacin kasar baki daya, a bayan da sojojin Malin suka ayyana juyin mulki cikin watan Maris na bara.

  Wakilin Muriyar Amurka a Gao yace galibin mayakan sakai dake can sun arce daga birnin tun cikin makon jiya lokacinda jiragen yakin Faransa suka fara kaiwa sansanonin mayakan sakan harin bama-bamai.

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye