Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Zabe A Isra'ila Ya Nuna Cewa Netanyahu Na Da Jan Aiki A Gabansa


Hoton Firayim Minista Isra'ila kennan, Benjamin Netanyahu yana dagawa magoya baya hannu a birnin Tel Aviv. Junairu 23, 2013.
Hoton Firayim Minista Isra'ila kennan, Benjamin Netanyahu yana dagawa magoya baya hannu a birnin Tel Aviv. Junairu 23, 2013.
A Isra’ila kwarya-kwaryar sakamakon zabe ya nuna cewa gamayyar jam’iyyu masu ra’ayin rikau, da masu sassaucin ra’ayi sun raba kujeru da suke majalisar dokokin kasar , sakamakon da ya bada mamaki, al’amari kuma da yanzu zai tilastawa Firayim Minista Netanyahu aiki tukuru domin kafa gwamnati.

Bayan an kammala kidaya kashi 99 cikin 100 na kuri’u da aka kada a zaben, ko wani bangare ya kama kujeru 60 cikin kujeru 120 da suke majalisar dokokin kasar da ake kira Knesset.

Jam’iyar Likud mai ra’ayin mazan jiya ta Firayim Minista Netanyahu, wacce take kawance da jam’iyyar Yisreal Beitenu suna kan gaba da kujeru 31, wanda ya nuna sun sami komawa baya da kujeru 11, idan aka kwatanta da 42 da suka samu a zaben da aka yi a baya.

Za a umarci PM ya kafa gwamnati, lamarin da zai kara yi masa wuya ganin nasarar ba-zata da masu sassaucin ra’ayi suka samu.

A halin da ake ciki kuma, yau ne ‘yan kasar Jordan suke zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, a zaben da ‘yan hamayya suka kauracewa, domin suna zargin cewa sauye sauye kan zabe da aka gudanar a bara, suna taimakawa magoya bayan sarki Abdullah.

Masu zaben zasu zabi wakilai 150 na majalisar wakilan kasar. Akwai majalisar dattijai mai wakilai 60, wadanda sarki Abdullah ne yake nada su.
XS
SM
MD
LG